Dillalin Paul Pogba, Mino Raiola yace ‘Dan wasansa 'bai jin dadi' zai bar Kungiyar Man Utd
- Akwai yiwuwar cewa Paul Pogba ba zai shekara a Manchester United ba
- Dillalin ‘dan wasan ya ce Pogba ba ya jin dadin zaman da yake yi a yanzu
- Jamie Carragher ya soki Mino Raiola, ya bada shawarar a saida Tauraron
Ta tabbata cewa ‘dan wasa Paul Pogba bai jin dadin zamansa a kungiyar Manchester United, kuma zai bar kungiyar a karshen kakar shekara mai zuwa.
Sky Sports ta ce dillalin ‘dan kwallon na kasar Faransa, Mino Raiola ya bayyana wannan a lokacin da ya yi hira da Tuttosport a cikin farkon makon nan.
Raiola ya ce tauraron ya na bukatar ‘canjin iska’, don haka ya ba kungiyar Manchester United shawarar ta rabu da ‘dan kwallon ko kuma ya tashi a bagas.
"Paul bai jin dadin Man Utd, bai iya fito wa yayi abin da ya ga dama ko abin da mutane za su so.”
KU KARANTA: Pogba ya na da COVID-19
Dillalin ya cigaba da cewa: “Yana bukatar ya canza kungiya, ya na bukatar ‘canjin-iska. Ya sa hannu a kwantiragin da zai kare a kakar shekarar 2022...”
Raiola ya ce: “Amma abin da yafi wa kowa shi ne a rabu a kakar shekara mai zuwa.” Idan aka jira sai nan da shekara daya da rabi, za a samu Pogba kyauta.
Kafin yanzu kocin Manchester, Ole Gunnar Solskjaer ya nanata cewa Pogba ba zai je ko ina ba.
Amma tsohon ‘dan wasan Liverpool, Jamie Carragher ya yi kaca-kaca da dillalin ‘dan wasan mai shekara 27, sannan ya ba Manchester shawara ta saida shi.
KU KARANTA: Pogba ya yi magana game da addinin musulunci
Jamie Carragher ya na ganin ana zuzuta Pogba wanda ya ci kwallo daga dawowarsa daga jinya.
Kwanaki kun ji ana ta rade-radin Paul Pogba ba zai kara bugawa kasarsa kwallo ba saboda kalaman da shugaban Faransa ya yi a kan addinin Islama.
Daga baya ‘Dan wasan mai shekara 27 wanda ya buga wa Faransa wasanni 72 ya musanya maganar, ya yi barazanar shiga kotu da masu yada jita-jitar.
Tsohon 'dan wasan Juventus, Pogba, ya na ganin wasu gidajen jaridu ba su yin abin da ya dace wajen buga labarai, tauraron ya bayyana haka ne a Twitter.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng