Gaskiyar zance: Paul Pogba ya bayyana muhimmancin addnin Musulunci a wajensa

Gaskiyar zance: Paul Pogba ya bayyana muhimmancin addnin Musulunci a wajensa

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Labile Pogba ya bayyana cewa ala dole ya fara daukan addinin Musulunci da muhimmanci tun bayan daya fahimci cewa ita kadaice addinin dake bashi zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Legit.ng ta ruwaito a farkon rayuwarsa Pogba ba Musulmi bane, duk kuwa da cewa mahaifiyarsa Musulma ce, daga bisani ne ya fara gudanar da bincike akan addinin, wanda hakan ya kaishi ga rungumar addinin, kuma ta canza masa rayuwa.

KU KARANTA: APC ta tsayar da mutumin daya saci sandan majalisa a matsayin mataimakin shugaban majalisa

Pogba ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da jaridar United Xtra inda yace “Addinin Musulunci shine komai a wajena, wannan shine yasa nake godiya ga Allah, Musulunci ya sauya min rayuwa, tasa na fahimci abubuwa da dama a rayuwa.

“Addinin ya bani kwanciyar hankali da natsuwa matuka, naji dadin sauyin dana samu a sakamakon Musulunci musamman duba da cewa ba’a a Musulunci aka haifeni ba, duk da cewa mahaifiyata Musulma ce.

“Yadda ake ganin Musulunci kamar addinin yan ta’dda ne ba haka yake ba, duk abinda kuke gani a kafafen watsa labaru duk bashi bane Musulunci, ina, addinin Musulunci abu ne mai kyau, idan har ka binciki addinin, zaka fahimceshi yadda ya kamata.” Inji shi.

Kowa a cikin watan Ramadana sai da Pogba tare da abokinsa Zouma suka ziyaraci kasar Saudiyya inda suka gudanar da aikin Umarah, sai dai ba wannan karon bane farau a wajensa ba, ya kasance yana zuwa akai akai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel