Pogba ya kamu da COVID-19

Pogba ya kamu da COVID-19

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon ƙafa ta Manchester United, Paul Pogba ya kamu da cutar coronavirus.

Cocin tawagar kasar Faransa, Didier Deschamps ya tabbatar da cewa an cire Pogba daga tawagar kasar bayan gwajin ya nuna ya kamu da ƙwayar cutar.

An maye gurbin Pogba da Eduardo Camavinga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Pogba ya kamu da COVID-19
Pogba ya kamu da COVID-19
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: An naɗa ɗan Najeriya Ministan Shari'a a Canada (Hotuna)

Hakan na nufin Pogba zai shafe kwanaki 14 a killace - ma'ana ƙungiyarsa ta Manchester za ta fara shirye-shirye kakar wasa ta 2019-20.

Rashin Pogba zai bawa matashin ɗan kwallo kamar Camavinga damar nuna bajintar sa.

A wani labarin Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa zakaran kungiyar Barcelona, Lionel Messi ya ce zai bar kungiyar ta Barcelona kuma ya zaɓi ya koma Manchester City a cewar Marcelo Bechler.

An fara jita-jitar cewa Messi baya jin dadin zamansa a kungiyar ta Barcelona tun bayan mummunan kayen da kungiyar ta sha a hannun Bayern Munich a wasan kusa da na karshe na gasar ƙwararru wato Champions League.

Bayern Munich ta lallasa Barcelona 8 - 2 a wasan wadda hakan abu ne mai ciwo ga babban kungiya kamar Barcelona.

Zakaran ɗan kwallon mai shekaru 33 ya aike wa Barcelona da wasikar fax inda ya bayyana musu cewa yana son barin ƙungiyar.

Duk da cewa kwangilar sa zai kare ne a 2020-21, Messi da lauyoyinsa suna ganin akwai wata dama cikin yarjejeniyar da za ta bashi ikon barin ƙungiyar kafin lokacin.

Marcelo Bechler shine ɗan jaridar da ya fara fitar da labarin cewa Messi yana son barin Barcelona a cikin kwana kwanan nan.

Ana yi wa Bechler kallon sahihin majiya a kan batutuwan da suka shafi Barcelona kuma shine ɗan jarida na farko da ya wallafa labarin cewa Neymar zai bar kungiyar zuwa Paris Saint-German a 2017.

A cewar Bechler, Messi da tsohon manajan sa suna tattauna a kan batun komawar - kuma ana ganin Manchester City a shirye ta ke domin ganin nasarar hakan.

Ana ganin Messi yana sha'awar irin salon kwallon ƙafa da Manchester City ke buga wa.

Bechler ya ce a halin yanzu babu tabbas kan abinda ka iya faruwa saboda rashin jituwa tsakanin ɗan wasa da kungiyarsa da kuma ko akwai yiwuwar ya bar kungiyar kafin wa'adin yarjejeniyar sa ta cika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel