Kungiyar RIPAN ta yarda ta karya kudin buhun shinkafa ya kai N19, 000
- Kungiyar RIPAN ta yarda ta yi kasa da farashin buhun shinkafa
- ‘Yan kasuwan zasu yi haka ne domin rage radadin da aka shiga
- Ana sa ran a koma saida buhu a kan N19, 000 cikin Disamban nan
Kungiyar RIPAN ta masu aikin shinkafa a Najeriya ta amince ta rage farashin shinkafa ta yadda za a rika sayen kowane buhu a kan N19, 000.
Jaridar Daily Nigerian ta samu labari a makon nan cewa a halin yanzu ana saida kilogram 50 na buhun shinkafa tsakanin N28, 000 da N30, 000.
Rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana cewa kungiyar RIPAN za ta karya farashin buhun shinkafa ne a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020.
Wannan mataki yana zuwa ne bayan farashin kayan abinci sun tashi a sakamakon rufe iyakoki da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi.
KU KARANTA: Bincike ya nuna Buhari bai bi doka da zai zabi Shugabar NAPTIP ba
Tun daga lokacin da aka hana shigo da shinkafa, wasu ‘yan kasuwa suna ta sayen buhuna rututu, suna adana wa da nufin su samu kazamar riba.
Kungiyar RIPAN ta hada kai da babban bankin kasa na CBN a farkon makon nan ta kafa wani kwamiti da zai yi kokarin ganin an samu sauki.
Shugaban kamfanin aikin shinkafa na Tiamin, Aminu Ahmed shi ne zai jagoranci wannan aiki na tabbatar da cewa an rage farashin shinkafar.
A wata hira da ya yi da jaridar, Ahmed ya tabbatar da cewa sun amince su rage farashi zuwa N19, 000 domin taimakawa gwamnati na rage radadi.
KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da aikin da zai sa a daina dauke wuta a Jami’ar FUAM
Aminu Ahmed yace masu gyaran samfarera sun karya farashinsu zuwa N160 a kan kowane kilogram, wannan zai sa ainihin buhun ya rage kudi.
A ranar Alhamis ne wani tsagera ya tare ‘Dan Majalisa mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya bukaci sai ya bada kudi har Naira miliyan biyu.
Sabon Sanatan na jam'iyyar APC ya tsira daga hannun wannan mutumi da ya nemi ya bindige sa. Wani hadimin Sanatan ya bayyana haka a wani jawabi.
Yanzu haka ana binciken wannan mutumi yayin da Sanatan yace laifin zaman kashe wando ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng