Kyau da kwakwalwa: Hotunan sarakunan gargajiya mata 7 a Najeriya
- A Najeriya, maza ne kadai suke hawa kujerun sarauta idan iyayensu sun mutu
- A wasu kabilun kuma mata sukan hau na rikon kwarya, kuma basu wuce watanni 6
- Labarin nan ya kun shi sarakuna mata guda 7, kabilu daban-daban wadanda suka zarce watanni 6 a sarauta
Sarauta a Najeriya yawanci ta maza ce, saboda yanayin karfin iko, izza da kuma hulda da jama'a. Yawanci akan hana mata sarauta ne saboda rauninsu.
Sannan akwai kabilun da suke baiwa mata sarauta, sai dai ta rikon kwarya ce, ba a so su wuce watanni 6. Kuma sarauta tana hana mace aure, matsawar ta hau mulki ba za tayi aure ba, kuma ba za ta haihu ba.
A rubutun nan, akwai labarin sarakuna mata 7, wadanda suka zarce watanni 6 a karagar mulki.
1. HRM Moyinoluwa Olubunmi Falowa
Ta hau sarautar rikon kwaryar shugabar Ibule da ke karamar hukumar Ifedore a jihar Ondo. Ta gama jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Ondo. Ta amshi mulkin ne a watan Afirilun 2019, bayan rasuwar mahaifinta.
Za ta cigaba da mulki har sai an nada wani sabon sarkin.
2. HRM Taiwo Oyebola Agbona
An nada ta a 2017 da nufin har sai an samu wani sarki namiji wanda zai hau kujerarta. Legit.ng ta tattaro bayanai a kan yadda aka nada ta kasancewarta diyar sarkin ta farko. Mahaifinta ya mutu a ranar 4 ga watan Mayun 2017. Ta gama jami'ar Achievers da ke Owo.
KU KARANTA: Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta
3. HRM Tinuade Babalola Adejuiyegbe
Ita ce Oluborapa ta Ibroropa da ke Akoko jihar Ondo. Ta hau mulki a ranar 23 ga watan Fabrairun 2015 bayan mutuwar mahaifinta.
Lokacin da ta hau mulki tana kasa da shekaru 20, sannan bata gama jami'ar Adekunle Ajasin ba. Ta gama jami'ar a 2018, kuma ta yi bautar kasa a 2019, inda ta zama basarakiya ta farko da tayi hakan saboda shekarunta 22 kacal.
4. HRM Elizabeth O.T. Orogun
HRM Elizabeth mai rikon kwaryar sarautar Akunu Akoko ce a jihar Ondo.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2, sun cafke 'yan fashi a Sokoto
5. HRM Adekemi Omorinbola
Basarakiyar Asin ta Iwara-Oka Akoko da ke jihar Ondo. Tana kasa da shekaru 20 ta hau karagar mulkin, don ko makarantar sakandare bata gama ba a lokacin.
Ta gaji mahaifinta a ranar 9 ga watan Janairun 2010. Ta cigaba da karatunta a jami'ar jihar Ekiti, duk da sarautar. An zabe ta tayi mulkin duk da ita ce auta cikin yaran sarkin guda 6 duk mata.
6. HRM Princess Damilola Falegan
Ita ce ta gaji sarautar Irese, Onirese ta masarautar Irese, a karamar hukumar Ifedore da ke jihar Ondo. Ta cika shekara 25 a duniya a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020.
7. HRM Tejumade Falade Adeboye
Ita ce Odopetu ta masarautar Akure. Ta sauka daga mulkin bayan tayi aurenta. Ta yi shagalin zagayowar shekarar aurenta 1 a ranar 7 ga watan Nuwamba.
A wani labari na daban, daukaka karar da Maryam Sanda tayi na babbar kotu, a kan kisan mijinta da ake zargin ta yi a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, shi ya fara janyo cece-kuce a Najeriya.
Kwamitin bincike na mutum 3, wanda Alkali Stephen Ada ya jagoranta, ta kori daukaka karar Sanda a ranar Juma'a.
Idan ba a manta ba, ana zargin Sanda da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda da ne ga dan uwan tsohon shugaban jam'iyyar PDP.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng