Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu

Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu

- Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kaiwa gwamnan jihar Legas ziyara ta musamnan

- Sakataren yada labaran gwamnan ne ya wallafa bidiyon ziyarar a shafinsa na Twitter

- Ya ce sarkin yayi magana a kan bukatar 'yan Najeriya su hada kawunansu saboda zaman lafiya

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai wa gwamnan jihar Legas ziyara ta musamman a ranar Lahadi. Sarkin ya hadu da gwamnan a gidan gwamnatin jihar Legas dake Marina.

Sakataren yada labaran Gwamna Sanwo-Olu, Gboyega Akosile ya wallafa bidiyon ziyarar da sarkin ya kai wa gwamnan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarsa, basaraken ya yi magana a kan bukatar 'yan Najeriya su hada kawunansu, sannan ya bukaci kowa ya kwantar da hankali domin samun wanzuwar zaman lafiya.

Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu
Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu. Hoto daga @MasarautarKano
Asali: Twitter

Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu
Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu. Hoto daga @MasarautarKano
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa

Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu
Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu. Hoto daga @MasarautarKano
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi

Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu
Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu. Hoto daga @MasrautarKano
Asali: Twitter

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta musanta labarin da yayi ta yawo a yanar gizo na tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, cewa ya tura wa shugaba Buhari N12,500,000 zuwa asusunsa lokacin yana gwamna.

Rahotonnin sun yi ta yawo da safen nan wanda ake cewa gwamnan ya tura wa Shugaba Buhari kudin cikin asusunsa.

A wata takarda da babban hadimin shugaban kasa na musamman a kan harkar yada labarai, Garba Shehu ya saki da yamman nan, ya musanta rahoton.

A cewarsa, an tura kudin ne a asusu mai suna Muhammadu Buhari estate, wanda mallakin gwamnatin ne ba na Shugaba Buhari ba kamar yadda ake zargi.

"Wannan labarin bogi ne. Wata takarda ta nuna yadda aka tura N12,500,000 daga asusun jihar Ogun, zuwa 'PMB Estate' duk don a bata suna Shugaba Muhammadu Buhari.

"PMB Estate wani babban rukunin gidaje ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Shugaba Buhari ne ya gina gidajen bayan ya kai wa jihar ziyara," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel