Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa

Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa

- Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu ya dakatar da shugaban ma'aikatansa

- Hakan ya biyo bayan ganinsa a wani bidiyo yana lika wa wani fasto kudi, yana kwasar rawa

- Bayyanar bidiyon ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya dakatar da shugaban ma'aikatansa, Anthony Agbazuere.

Bayan bayyanar bidiyon Agbazuere yana watsa wa Odumeje, 'Indaboski', kudi ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, The Cable ta ruwaito.

A bidiyon an ga Agbazuere yana manna wa Chukwuemeka Ohanaemere wanda aka fi sani da Odumeje, wannan sanannen faston na Onitsha, yana kwasar rawa.

Duk da dai ba a san lokacin da aka dauki bidiyon ba, amma ko da gani Agbazuere yana kujerarsa.

Jama'a sun dinga caccakrsu inda suka kalla hakan a matsayin almubazzaranci.

A wata takarda ta ranar Lahadi, Chris Ezem, sakataren gwamnan, inda aka tabbatar da dakatar da CoS take-yanke. Kamar yadda takardar tazo:

"Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, ya umarci dakatar da shugaban ma'aikatan gwamnan daga ofishinsa, Dr ACB Agbazuere."

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi

Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa
Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa. Hoto daga pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda

A wani labari na daban, wani bidyo da yake nuna shugaban ma'aikatan fadar gwamna jihar Abia, Anthony Agbazuere yana zuba wa wani fasto mai suna Odumeje wanda aka fi sani da Indaboski ya janyo cece-kuce.

A bidyon da wani mai suna Enwagboso ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga Agbazuere yana watsa wa Chuwuemka Ohanaremere wanda aka fi sani da Odumeje kudi.

A bidiyon, ba a ga wacce rana lamarin ya faru ba, amma ya bayyana cewa a ofishin Agbazuerre ya faru, Channels Tv ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: