Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27

Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27

- Jaruma Rahama Sadau ta mika godiyarta ga Ubangiji da ya albarkace ta da kara shekara daya a rayuwarta

- Rahama ta bayyana cikarta shekaru 27, a ranar 7 ga watan Disamba, ga masoyanta da masu bibiyarta a kafafen sada zumunta

- Ta wallafa hotunanta masu kayatarwa, cike da farin cikin da annashuwar ganin wannan babbar ranar ta rayuwarta

Jarumar fina-finai, Rahama Sadau, tana da dalilai masu yawa da za ta godewa Allah da ya bata ikon kara shekara daya a duniya.

A ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, jarumar ta cika shekaru 27 da haihuwa kuma ta wallafa labarin ga mabiyanta da masoyanta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Baya ga annobar coronavirus da ta lalata tattalin arzikin duniya, jarumar ta bayyana cigaba da nasarorin da ta samu a shekarar nan.

Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27
Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27. Hoto daga Rahama_Sadau
Asali: Instagram

KU KARANTA: Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa

Ta ce cikin kalubalen da ta fuskanta a wannan shekarar har da hotonta da ya janyo cece-kuce iri-iri kwanakin baya.

Ta ce hoton ya janyo mata caccaka ta kowanne kafar sada zumunta. Yanzu kuwa kamar an yi ruwa an dauke.

Hakika samun nasarar damar jure wannan caccakar, babbar dama ce da Ubangiji ya bata.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa

A wani labari na daban, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai wa gwamnan jihar Legas ziyara ta musamman a ranar Lahadi. Sarkin ya hadu da gwamnan a gidan gwamnatin jihar Legas dake Marina.

Sakataren yada labaran Gwamna Sanwo-Olu, Gboyega Akosile ya wallafa bidiyon ziyarar da sarkin ya kai wa gwamnan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarsa, basaraken ya yi magana a kan bukatar 'yan Najeriya su hada kawunansu, sannan ya bukaci kowa ya kwantar da hankali domin samun wanzuwar zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng