NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a

NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a

- Shugaban NAAT ya ce ba za su amince kungiyar ASUU ta raba naira biliyan 40 da FG ta amince da biyansu su kadai ba

- Ya ce NAAT tana bukatar naira biliyan 100, sannan FG ta biya su naira biliyan 5 duk shekara na tsawon shekaru 5

- Sannan ita ta gabatar da nata salon biyan albashin, UGPPPS, don tana cutuwa da IPPIS din da FG ta gabatar mata kwarai

NAAT ta ja kunnen gwamnatin tarayya a kan amincewa da salon biyan albashi da ASUU ta gabatar na UTAS, Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce kada gwamnati ta yarda wata kungiya ta dinga juya ta yadda ta ga dama, ta hanyar amincewa da salon biyan malaman jami'a. Ta ce NAAT ta samar da nata salon biyan albashin na TIIPS.

Idan ba a manta ba, SSANU da NASU ba su dade da sanar da gwamnatin tarayya cewa sun kirkiri nasu salon biyan albashin ba, wanda zai maye gurbin IPPIS, wanda gwamnatin tarayya ta gabatar.

Sabon salon biyan albashin da SSANU da NASU suka gabatar shine UGPPPS.

NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a
NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi

Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma ne ya tattauna da manema labarai bayan taron NEC na 44, wanda aka yi cikin kwanakin karshen mako, inda yace kungiyarsu ba za ta amince wata kungiya ita kadai da 'yan cikinta su raba naira biliyan 40 da gwamnatin tarayya ta amince da bayarwa kwanakin da suka gabata ba.

Ya kara bayyana yadda har yanzu kungiyarsu take bin gwamnatin tarayya naira biliyan 71 tun 2009.

Kamar yadda yace, NAAT tana bukatar naira biliyan 100 take-yanke, sannan gwamnati ta dinga biyan naira biliyan 5 duk shekara, na tsawon shekaru 5 masu zuwa, don a gyara wuraren gwaje-gwaje da sauransu na jami'o'in kasar nan don a samu ilimi mai inganci kamar na kasashen ketare.

Shugaban kungiyar ya caccaki shugaban kwamitin cigaba da sasanci na tarayya, Farfesa Munzali Jibrin, a kan maganar da yayi a kan raba kudaden shiga, inda yace tsohon sakataren NUC ya zama bakin ASUU.

KU KARANTA: Zargin damfarar N2.2b: Kotu ta ba tsohon gwamna damar fita kasar waje neman lafiya

Yace an horar da 'yan kungiyar NAAT ne musamman don koyar da ilimi a aikace, amma basu samu damar hakan ba, shiyasa suke wahala wurin koyarwa.

Yayi kira akan inganta kayan koyarwarsu na jami'o'i, inda yace don sun kushi UTAS baya nufin sun amince da IPPIS.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tarba sojoji daga Kamaru a ranar Alhamis.

Sojojin sun isa gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar. A taron, gwamnan ya bukaci sojojin Kamaru da su taimaka wurin kawo karshen 'yan ta'addan Boko Haram, jaridar Punch ta wallafa.

Kwamandan rundunar soji na 4, Janar Saly Mohammadou, ya jagoranci sojojin Kamaru zuwa gidan gwamnatin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel