Zargin damfarar N2.2b: Kotu ta ba tsohon gwamna damar fita kasar waje neman lafiya

Zargin damfarar N2.2b: Kotu ta ba tsohon gwamna damar fita kasar waje neman lafiya

- Babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta amince wa Fayose tafiya kasar waje don neman lafiya

- Idan ba a manta ba, EFCC ta maka Foyose kotu bisa zarginsa da damfarar naira biliyan 2.2

- Alkalin ya amince da bukatarsa, ya kuma dage sauraron shari'ar zuwa 22 ga watan Janairun 2021

Babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta amince wa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ake zargin damfarar naira biliyan 2.2, ya tafi kasar waje neman lafiya.

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya amince da bukatar da lauyansa, Ola Olanipekun (SAN), wanda ya bukaci kotu ta amince yayi tafiyar.

EFCC, ta lauyanta Rotimi Jacobs (SAN), bai kalubalanci bukatar Fayose ba, Channels TV ta wallafa hakan.

Mai shari'a Aneke ya dage shari'ar zuwa 22 ga watan Janairun 2021. EFCC ta maka Fayose da wani kamfani, Spotless Investment Limited, a kotu ne bisa zargin damfarar naira biliyan 2.2.

Zargin damfarar N2.2b: Kotu ta ba tsohon gwamna damar fita kasar waje neman lafiya
Zargin damfarar N2.2b: Kotu ta ba tsohon gwamna damar fita kasar waje neman lafiya. hoto daga @ChanneTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

Cikin abubuwan da EFCC take zargin Fayose sun hada da kwasar N1,219,000,000 don yin amfani dasu wurin yakin neman zaben gwamnoni na 2014, wanda ya kwashi kudin a ranar 17 ga watan Yuni na 2014.

Sannan ana zargin tsohon gwamnan da amsar $5,000,000 daga hannun Sanata Musiliu Obanikoro, sai kuma wasu kudaden daga hannun karamin ministan tsaro a jihar.

Sannan EFCC ta zargi Fayose da siyan wani wuri a Abuja, No. 44 Osun Crescent, Maitama da ke Abuja, na naira miliyan 200 da sunan yayarsa, Mrs Moji Oladeji.

KU KARANTA: Yadda soja mace ta dinga zabga wa gurgu mari a kan ya tsawatar wa yaron ta

A wani labari na daban, kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Alkali Yusuf Halliru ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020, jaridar The Cable ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel