Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi

Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi

- Fadar shugaban kasa ta musanta labarin cewa gwamnatin jihar Ogun ta tura wa Shugaba Buhari N12,500,000

- A cewar kakakin Buhari, Garba Shehu, an tura kudin ne cikin asusu mai suna "PMB Estate", wanda mallakin gwamnatin Ogun ne

- A cewarsa, masu yada labarin suna yi ne don su bata sunan Buhari, wanda yayi fice wurin yaki da cin hanci da rashawa

Fadar shugaban kasa ta musanta labarin da yayi ta yawo a yanar gizo na tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, cewa ya tura wa shugaba Buhari N12,500,000 zuwa asusunsa lokacin yana gwamna.

Rahotonnin sun yi ta yawo da safen nan wanda ake cewa gwamnan ya tura wa Shugaba Buhari kudin cikin asusunsa.

A wata takarda da babban hadimin shugaban kasa na musamman a kan harkar yada labarai, Garba Shehu ya saki da yamman nan, ya musanta rahoton.

Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi
Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ikirarin tura wa Buhari kudi asusunsa da jihar Ogun ta yi. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

A cewarsa, an tura kudin ne a asusu mai suna Muhammadu Buhari estate, wanda mallakin gwamnatin ne ba na Shugaba Buhari ba kamar yadda ake zargi.

"Wannan labarin bogi ne. Wata takarda ta nuna yadda aka tura N12,500,000 daga asusun jihar Ogun, zuwa 'PMB Estate' duk don a bata suna Shugaba Muhammadu Buhari.

"PMB Estate wani babban rukunin gidaje ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Shugaba Buhari ne ya gina gidajen bayan ya kai wa jihar ziyara.

"PMB Estate mallakin gwamnatin jihar Ogun ne, amma an sanya wa wurin suna ne don girmama Shugaban kasa, ba don ya mallaki wurin ba.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 12, sun cafke wasu 26 a Katsina

"Kada a amince da duk wasu labaran bogi da ke yawo don bata sunan shugaban kasa, wanda yayi fice a yaki da rashawa," yace.

A baya Muhammadu Buhari yana amsar fansho na kasancewarsa soja, bai taba sanya wa wani kamfani sunansa ba.

Mun kuma tattauna da ma'aikacin da ya sanya alamar biyan kudin a Twitter. Ya yi aiki a lokacin gwamna Amosun.

Ya tabbatar da cewa an tura kudin ne daga asusun kudin shigar jihar Ogun, zuwa na PMB Estate, saboda wasu ayyuka da aka yi wa gidajen. Amma hakan bashi da wata alaka da Shugaba Muhammadu Buhari.

A wani labari na daban, Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Alhamis, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa, Lt. Janar Tukur Buratai, a kan yadda yace ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 a Najeriya.

The Punch ta ruwaito yadda shugaban sojin kasa yayi wata magana bayan 'yan kwanaki da 'yan Boko Haram suka kashe manoman shinkafa 43 a jihar Borno.

Tsohon sanatan ya mayar da martani a kan maganar, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Alhamis, inda yace kalaman Buratai suna nuna karewar basira da rashin dabarun yaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel