Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi

Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi

- A makon daya gabata ne rahotanni su ka wallafa labarin cewa wata jami'ar kasar Amurka ta dauki gwamna Ganduje aiki a matakin Farfesa

- Sai dai, daga bisani jami'ar ta fito ta musanta hakan tare da bayyana cewa ba ta da masaniya a kan batun

Gwamnatin jihar Kano a ranar Lahadi ta buƙaci hukumar jami'ar West Carolina ta nemi afuwar gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan naɗin mukamain Farfesa mai cike da sarƙaƙiya, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewa Jami'ar ta nada Ganduje muƙamin babban malami da zai koyar da ilimin harkokin ƙasashen ƙetare da da gwamnatin zamani(e-governance) a matakin cikakken Farfesa.

A cikin wani jawabi da sakataren gwamnatin jihar Kano, Usman Alhaji, ya fitar, ya yi kira da a tsawatarwa da masu jami'ar da suka haddasa cece-kucen da ya tozarta mai girma gwamna.

KARANTA: Yaba kyauta: Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza, ta bayar da adireshin shafin yanar gizi

Usman Alhaji ya ce gwamna Ganduje ko wani jami'in gwamnatinsa basu da wani dalilin da zai kawo shakku ga wasiƙar da ɗaya daga cikin malaman gundumar ya aiko ta hanyar amfani da kayan ofishin jami'ar.

Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi
Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi @dawisu
Asali: Twitter

"Mun yi baƙin ciki marar misaltuwa sakamakon yamutsa hazo da cece-kucen da wannan naɗi mai cike da sarƙakiya ya jawo."

"Wannan naɗin an yi shi ne don cin mutunci da tozarta mai girma gwamna da mutanen kirkin jihar Kano", kamar yadda jawabin ya yi ƙarin haske.

Usman Alhaji ya nuna cewa Ganduje ya samu takardar shaidar karatun ilmi ta ƙasa (NCE) a 1972, shaidar Digiri a fannin ilmin kimiyya daga jami'ar Ahmadu Bello, Zaria a 1975.

KARANTA: Zai iya kara aurar wasu matan; jarumar fim da ta auri daya daga cikin attajiran Nigeria

Sai shaidar karatun digirin digirgir; ɗaya a fannin nazarin ilmi daga Jami'ar Bayero Kano a 1979, ɗaya kuma daga fannin kula da harkar jama'a daga jami'ar Ahmadu Bello 1985.

Daga nan kuma ya yi Digirinsa na uku a jami'ar Ibadan da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Sakataren yace a halin da ake ciki yanzu, gwamna Ganduje ne zai zama mutum na ƙarshe a duniya da zai karɓi ko ya nemi a naɗa shi muƙamin da ya shafi koyarwa a ciki ko wajen Najeriya.

A yayin da yake yi wa jami'ar fatan alkhairi, jawabin nasa ya nuna kaɗuwa dangane da saƙon cikin wasiƙar wadda tazo daga ofishin babban mataimakin shugaban jami'a akan harkokin koyarwa.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa a ranar Juma'a ne tsohon gwamna jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC ya ziyarci jihar Kano

Ya ziyarci jihar Kano ne domin halartar daurin auren diyar babban Malamin addinin Islama, Sheikh Bin Usman.

Sai dai, bayan ziyarar ta sa, kafafen yada labarai sun yada cewar kungiyar malaman jihar Kano ta goyi bayan takarar Tinubu a shekarar 2023, lamarin da ya bar baya da kura.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng