Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyawa takarar Tinubu baya a 2023

Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyawa takarar Tinubu baya a 2023

- A ranar Juma'a ne tsohon gwamna jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC ya ziyarci jihar Kano

- Ya ziyarci jihar Kano ne domin halartar daurin auren diyar babban Malamin addinin Islama, Sheikh Bin Usman

- Sai dai, bayan ziyarar ta sa, kafafen yada labarai sun yada cewar kungiyar malaman jihar Kano ta goyi bayan takarar Tinubu a shekarar 2023

Majalisar Shura ta malaman jihar Kano ta ƙi amincewa a kan cewa ta yarje tare da marawa jagoran jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, baya a kan kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai gabatowa na shekarar 2023.

Shugaban majalisar malaman, Sheikh Ibrahim Khalil, shine ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano a ranar Lahadi, kamar yadda The Nation ta rawaito.

In zaku iya tunawa Bola Ahmed Tinubu ya shigo garin Kano ranar Juma'a inda ya halarci ɗaurin auren ɗiyar Sheik Muhammad Bn Usman.

KARANTA: Farfesa Ali Garba na BUK ya rasu kwana biyu bayan neman addu'a wurin jama'a

Malam Khalil, wanda ya bayyana mamakinsa ƙarara da rahotannin da ƴan jarida suke fitarwa akan cewa Malaman Kano sun yarje tare da amincewa da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023.

Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyawa takarar Tinubu baya a 2023
Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyawa takarar Tinubu baya a 2023 @Solacebase
Source: Twitter

Ya bayyana cewa irin wannan labarin na iya haddasa rigima da rikici tsakanin malaman addinin Musulunci sakamakon saɓanin da mabambantan ra'ayin siyasa da zaɓi.

Ya ce,"Bola Tinubu ya zo Kano ne don halartar ɗaurin auren ɗiyar Sheik Muhammad Bn Usman."

"Daga nan sai taron ƴan siyasa magoya bayan Buhari a gidan Mumbayya sai kuma bangajiya ga wasu ƙungiyoyin musulmi da suka kai masa ziyara shi da Oba na Legas don yi musu jaje bisa dukiya da rayukan da aka rasa yayin zanga-zangar EndSARS"

"Wasu ƙungiyoyin musulmi sun ziyarci Bola Ahmed Tinubu da Oba na Legas bayan zanga-zangar EndSARS inda aka yaba masa bisa goyon bayan da ya bayar wanda yayi sanadiyyar ɗarewar Buhari karagar mulkin Najeriya a zaɓen 2015."

Ya ce dama Tinubu, cikin fara'a, ya ce zai rama ziyarar da aka kai masa, saboda bai taɓa tsammanin ziyarar ba, inda ya tabbatar cewa zai kawo irin wannan ziyarar.

KARANTA: Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza, ta bayar da adireshin yanar gizo ga ma su son ziyartar kasar

Malam Khalil ya ƙara da cewa "an sanar da shi ɗaurin auren ɗiyar Sheikh Muhammad Bn Usman wanda ya yi alƙawarin halarta."

"Duk da dai, yayin ziyarar, Tinubu ya ƙudiri aniyar ziyartar malamai wanda hakan ba zai yiwu a gare shi ba ya bi kowa har gidansa."

"Wane tudu wanne gangare wasu daga cikin malaman da suka kai ziyara Legas aka tattaro kansu zuwa inda Tinubu ya ziyarta tare da gwamna Abdullahi Ganduje."

"A nan ne ɗaya daga cikin malaman, Shehi Shehi, ya yi jinjina ga Tinubu bisa goyon bayan da ya bawa Buhari a shekarar 2015 wanda ya yi sanadiyyar samun nasararsa, inda ya ce koda yaushe zamu gode maka, kuma zamu rama irin karamcin da ka gwada mana."

"Abin dariya ne yadda gidajen jaridu ke faman yamaɗiɗin cewa wai malaman Kano sun yarda da kudirin Tinubu na takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023, wasu daga cikin malaman mu basa goyon APC, wasu kuma da suke APC ba shi suke marawa baya ba."

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, an dawo da wani tsohon bidiyo da shugaba Buhari ke zargin gwamnatin tarayya da zama babbar mai daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke takara, gabanin zaben shekarar 2015.

Dawo da bidiyon tamkar tuni ne ga shugaba Buhari domin ya tuna alakwuran da ya daukarwa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel