Mijina zai iya kara aurar wasu matan; jarumar fim da ta auri daya daga cikin attajiran Nigeria
- Fitatacciyar jarumar fina-finan kudancin Nigeria, Regina Daniels, ta ce ba ta da damuwa ko matsala idan mijinta ya na son kara auren wasu matan
- Regina ta na auren Ned Nwoko, daya daga cikin hamshakan attajiran 'yan kasuwa da Nigeria ke da su
- Tun kafin aurensu ake cece-kuce akan alakarsu da niyyarsu ta yin aure, musamman idan aka yi la'akari da banbancin shekarunsu
A wani cigaba da aka samu, fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Nigeria, Regina Daniels, ta bayyana cewa biloniyan mijinta, Ned Nwoko, zai iya ƙara auro wasu matan idan ya na son hakan, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
In zaku tuna, mijin nata kuma babban ɗan kasuwa a wata zantawa da aka yi da shi, ya ce matarsa Regina Daniels ta san da cewar zai iya ƙara auro wasu matan idan ya so.
Ned Nwoko ya yi bayanin yadda suka haɗu da Regina, inda ya ce basu taɓa haɗuwa kafin batun aurensu ba, sannan cikin sati uku da haɗuwarsu ta farko su ka yi aure.
KARANTA: Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai
Duk da kalaman Ned sun yamutsa hazon kafafen sadarwar zamani, sai dai matar tasa ta ce zaɓin mijinta ne idan ya so ya ƙara wasu matan, inda ta ce sam ba ta da damuwa ko matsala da hakan.
"Batu na gaskiya shine mijina zai iya ƙara auren wasu matan, hakan ba zai taɓa zamar min damuwa ko matsala ba" Kamar Regina yadda ta wallafa a shafinta na Tuwita.
A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Kamfanin sufurin jiragen sama na Arik Air ya sanar da zabge ma'aikata 300 sakamakon karayar tattalin arziƙi da ta samu kamfanonin sufurin jiragen sama sanadiyyar ɓarkewar annobar COVID-19.
A cewar manajan hulɗa da jama'a da yada labarai na Arik Air, Adebanji Ola, an ɗauki wannan matakin ne a ƙoƙarin da kamfanin ya ke don murmurewa tare da farfaɗowa don dawowa fagen fama da cigaba da ayyukan sufurin sama.
Sannan ga haraji mai ɗumbin yawa wanda ya ke haddasa tsadar aikinsu a halin da ake ciki yanzu.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng