Farfesa Ali Muhammad na BUK ya rasu kwana biyun bayan neman addu'a wurin jama'a

Farfesa Ali Muhammad na BUK ya rasu kwana biyun bayan neman addu'a wurin jama'a

- Jami'ar Bayero da ke Kano ta sake yin rashin babban malami, Farfesa Ali Muhammad Garba a ranar Lahadi

- Farfesa Ali ya rasu Kwanaki biyu kacal bayan ya wallafa, a shafinsa dandalin sada zumunta, cewa ya na neman addu'a a wurin jama'a

- Marigayin ya shiga jerin manyan malamai ma su mukamamin Farfesa da BUK ta rasa a cikin shekarar nan

Farfesa Ali Muhammad na sashen koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar BUK ya rasu, kamar yadda Legit.ng Hausa ta tabbatar.

A ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, ne Farfesa Ali ya wallafa cewa ya na neman jama'a su taya shi da addu'a saboda an kwantar da shi a asibiti.

Bayan ya yi sallama irinta addinin Musulunci a shafinsa na Facebook, Farfesa Ali ya bayyana cewa, "To, wankin hula ya kaimu dare.

"Bayan zazzafar muhawara da fada da kusan dukkan iyalina, an kwantar da ni a asibitin UMC Zahira da ke Kano.

KARANTA: Farfesa Yusuf Usman: 'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa

"Yanzu ba ni da halin yin mahawara ko musu koda ta hanyar latsa makulan kan wayata ta hannu.

"Ku taimaka, ku sakani a cikin addu'o'inku."

Marigayin ya shiga jerin Farfesoshi da jami'ar BUK ta rasa a cikin shekarar nan.

Daga cikinsu akwai Farfesa Haruna Wakili Wanda ya rasu a watan Yuni, Farfesa Monsuru Wanda ya rasu a watan Mayu, da kuma Farfesa Balarabe Maikaba wanda ya rasu a watan Afrilu.

Farfesa Ali Muhammad na BUK ya rasu kwana biyun bayan neman addu'a wurin jama'a
Farfesa Ali Muhammad na BUK ya rasu kwana biyun bayan neman addu'a wurin jama'a @AMHayatu
Source: Twitter

A ranar Lraba ne Legit.ng ta rawaito cewa tsohon babban darekta a hukumar NCAA (Nigerian Civil Aviation Authority), Kaftin Mukhtar Usman, ya rasu.

KARANTA: PDP ce kan gaba yayin da INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu

Kaftin Usman ya rasu a daren ranar Talata a Zaria bayan takaitacciyar rashin lafiya. Ya rasu ya na da shekaru 63 a duniya.

Punch ta rawaito cewa Ilitrus Ahmadu, shugaban wata kungiyar harkar sufurin jiragen sama, ya tabbatar mata da rasuwar Kaftin Usman da safiyar ranar Laraba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel