INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu

INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu

- Ranar Asabar, 6 ga watan Disamba, INEC ta tsayar domin kammala sauran zabukan maye gurbi a fadin Nigeria

- Zamfara da Bauchi da Legas na daga cikin jihohin da zaben mayen gurbi ya shafa kuma ake ganin za'a fafata tsakanin APC da PDP

- Sai dai, baturen zabe a jihar Zamfara, Farfesa Ibrahim Magawata, ya ce an soke zaben mazabu biyar a karamar hukumar Bakura

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC) ta bayyana zaben maye gurbi da ta gudanar ranar Asabar a jihar Zamfara a matsayin Wanda 'bai kammalu ba'.

A ranar Asabar, 6 ga watan Disamba, 2020, ne INEC ta gudanar da sauran zabukan maye gurbi a fadin Najeriya.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben ga manema labarai a ranar Lahadi, baturen zabe a Zamfara, Farfesa Ibrahim Magawata, ya ce za'a saka sabuwar ranar kammala zaben.

Magawata ya shaidawa manema labarai cewa ma'aikatan INEC na wucin gadi guda biyu sun bata, an nemesu an rasa, Kamar yadda Punch ta rawaito.

KARANTA: Sati guda bayan kisan manoma 43, mayakan Boko Haram sun kai sabon hari Banki

"An soke sakamakon zabe daga mazabu biyar a karamar hukumar Bakura. Za'a sanar da sabuwar ranar kammala zabe a mazabun da abin ya shafa," a cewar Farfesa Magawata.

INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu
INEC ta ce zaben maye gurbi a Zamfara 'bai kammalu ba' bayan bacewar ma'aikata biyu @Thecable
Source: Twitter

A cewarsa, akwai jimillar kuri'u 11,429 a mazabun da za'a sake zabe. Sakamakon da ke hannun INEC a halin yanzu ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Tudu, ya samu kuri'u 18,645 yayin da dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji, ya samu kuri'u 16,464.

KARANTA: Siyasar Kano: APC ta sauke shugabannin jam'iyyar ma su biyayya ga Ganduje

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa babban hafsan rundunar soji, Janar Tukur Buratai, ya gargadi anyan sojoji a kan juyin mulki.

Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, zama daram, a saboda haka lokacin katsalandan daga wurin sojoji ya wuce.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel