Buratai ya gargadi manya-manyan sojoji a kan juyin mulki

Buratai ya gargadi manya-manyan sojoji a kan juyin mulki

- Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan rundunar soji ya daurawa manyan sojoji 39 damarar kara girma zuwa manjo janaral

- A jawabin da ya gabatar a wurin, Buratai ya ce shugabancin rundunar soji ta na sane da cewa wasu 'yan siyasa na son ingiza manyan sojoji

- Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, ta zauna daram, an wuce lokacin da sojoji za su ke katsalandan cikin dimokradiyya

Babban hafsan rundunar sojoji, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya yi gargadi a kan juyin mulki tare da jaddada cewa rundunar soji ba zata lamunci duk wani yunkuri na kawo hargitsi da zai lalata tsarin dimokradiyya ba.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janaral, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

"Dimokradiyya ta zo kenan, ta zauna daram; har abada. Ba zamu yarda da duk wani yunkurin kawo hargitsi ba. Lokacin da sojoji za su ke tsoma baki a harkokin siyasa ya wuce, hakan ba zai kai mu ko ina ba. An wuce lokacin," a cewarsa.

KARANTA: Farfesa Yusuf ya fayyace irin dangatakar da ke tsakanin wasu gwamnonin arewa da 'yan bindiga

Buratai ya gargadi manya-manyan sojoji a kan juyin mulki
Buratai ya gargadi manya-manyan sojoji a kan juyin mulki @Premiumtimes
Asali: Twitter

Buratai ya bayyana cewa shugabancin rundunar soji ya na sane da cewa wasu 'yan siyasa su na son ingiza wasu manyan sojoji, amma, a cewarsa, ya yarda da tarbiyar sabbin manyan sojojin da suka samu kaein girma.

KARANTA: Matsalar Tsaron Najeriya ta fi ƙarfin Soja, in ji Gwamnoni

"Kar ku kulla hulda da 'yan siyasa. Kar ku nemi wani mukami ko alfarma daga wurin 'yan siyasa, idan ku na bukatar alfarma ku nema a wurin shugaban rundunar soji, shi kuma alfarmarsa ta na samuwa ne ta hanyar aiki tukuru da jajircewa da biyayya," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng