'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa

'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa

- Farfesa Yusuf Usman, tsohon shugaban hukumar NHIS ya ce akwai sanayya a tsakanin wasu gwamnonin arewa da 'yan bindiga

- A cewarsa, 'yan siyasa ne suka fara assasa matsalar 'yan bindiga da ta addabi jama'a a hallin yanzu

Wani tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa(NHIS), Farfea Yusuf Usman, a ranar laraba ya ce ƴan bindiga da suka addabi yankin arewacin Najeriya na da layukan kiran wayar gwamnonin yankin.

Ya bayyana ƴan siyasa a matsayin waɗanda suka fi ƴan bindiga hatsari da ɓarna sakamakon satar kuɗaɗen ƙasa su siyawa matasa bindigu don maguɗin zaɓe, sannan daga baya su yi watsi da su.

Malam Yusuf, wanda ya bayyana a gidan jaridar ARISE, ya ce a wasu lokutan, gwamnonin jihohin suna siyawa ƴan bindigar Shanu, sannan su basu kuɗi a matsayin hanyar tausar su.

"Da yawa daga cikin ƴan bindigar suna da layukan gwamnonin, suna kiransu. Nasan Nasir El-Rufa'i ya ƙi yin sulhu da su."

Gwamnoni na yin sulhu da su, su na siya musu shanu,suna siya musu kaji da tsuntsaye,dukkan wannan na nuni da gazawar gwamnati daga jihohin.

'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa
'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa "Kasan ire iren ƴan fashi kala biyu ne akwai ƴan fashin daji masu ɗauke da bindigu da kuma ƴan fashi masu yawa a gwamnati."

"Duk mutanen nan masu sace kuɗaɗen gwamnati sun fi ƴan bindiga hatsari. Dukkan ƴan siyasa masu satar kuɗi sun fi ƴan bindiga hatsari, kuma su na cin zaɓe."

Malam Yusuf yace rashin tsaron ƙasar nan ya samo asali ne saboda rashawa da azzalumar gwamnati.

"Ƴan siyasa sune masu shigo da muggan ƙwayoyi irinsu Tramol, su bawa matasa, su maida su ƴan daban siyasa. Suna basu makamai kuma da zarar an ci moriyar ganga, sai a yada korenta"

"Waɗannan yaran suna da bindigu, su na zama ƴan bindiga, ƴan daba, ƴan fashi, har ma ƙungiyar asiri ma, to kaga kenan ɓarayi sun sace kuɗi, su kuma ƴan bindiga suna karɓar kuɗaɗen fansa," a cewarsa.

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng