Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai

Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai

- Rahoto da dumi-dumi daga Newswire na nuni da cewa shugaba Buhari ya nuna rashin dadinsa a kan kwazon shugabannin rundunonin tsaro

- Mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro (NSA), Janar Babagana Monguno, ya ce Buhari ya kwankwashi shugabannin rundunonin a kan bukatar su kara dagewa

- Monguno ya ce Buhari ya umarci ofishinsa ya gana da gwamnonin yankin arewa maso yamma

Jaridar Newswire ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana mata cewa shugaba Buhari ya na cikin damuwa saboda jagwalewar harkar tsaro a Nigeria.

Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno, ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Newswire ta rawaito Monguno na cewa shugaba Buhari ya kwankwashi shugabannin rundunonin soji, ya bukaci su tashi haikan, su ninka kokarinsu.

KARANTA: Bidiyo: Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana yadda ake wulakanta Malamai idan sun je ganin Buhari domin yi ma sa nasiha

A cewar Monguno, duk da shugaba Buhari ya ce shugannin rundunonin su na iya kokarinsu, kokarin ya yi kadan wajen fuskantar kalubalen tsaro da kasa ke fuskanta.

Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai
Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai @Bashirahmad
Source: Twitter

Ya ce shugaba Buhari ya ce daga yanzu ba zai Kara karbar wani uzuri ba, kuma yana so su sauke nauyin da aka dora bisa wuyansu.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

Kazalika, Monguno ya bayyana cewa shugaba Buhari ya nuna rashin jin dadinsa a kan karancin hadin kai domin yin aiki tare a tsakanin hukumomin tsaron Najeriya wajen warware matsalar tsaro.

Monguno ya ce shugaba Buhari ya umarci ofishinsa ya gana da gwamnonin yankin arewa maso yamma da na jihar Neja domin tsara hanyoyin mayar da martani ga matsalar 'yan bindiga a jihohinsu.

A baya Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel