Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari

Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari

- A ranar Alhamis, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilai kwarara wadanda ya kamata a sauke shugabannin tsaro

- A cewarsa, shugaban kasa zai iya yi musu murabus, kamar yadda sauran ma'aikata suke yi, tunda duk sun fi shekaru 35 suna aiki

- Idan yana bukatar ayyukansu, zai iya daukansu a kujeru kamar minsitan tsaro, mai bayar da shawara a kan tsaro da sauransu

A ranar Alhamis, sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana yadda shugabannin tsaro suka dade a kan kujerunsu, inda yace ya kamata su tafi gida su huta, Daily Trust ta wallafa.

Kiraye-kiraye don cire shugabannin tsaro ya fara yawa ne tun bayan ganin yadda harkokin tsaro suka tabarbare a .

Sanatan ya roki fadar shugaban kasa, inda ya bukaci a sauya su da wasu, bayan kashe-kashen manoman shinkafa na Zabarmari a jihar Borno.

Tsohon ministan ilimi, kuma gwamnan jihar Kano wanda yayi mulki sau 2, bayan ganin kashe-kashen manoman Zabarmari, ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka bayyana, inda yace ya kamata a duba wannan shawarar.

KU KARANTA: Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki

Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari
Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Wannan wani gibi ne da gwamnatin tarayya bata cika ba. Kamar yadda doka ta tanadar, wajibi ne mutum ya kai shekaru 60 kafin ya ajiye aiki ko kuma ya yi aiki na shekaru 35," a cewarsa.

"Babu wani a cikinsu da yayi aiki kasa da shekaru 35. Shugaban ma'aikatan tsaro yayi shekaru 39 yana aiki. Duk sauran shugabannin sun zarce shekaru 60, ban da shugaban ma'aikatan tsaro mai shekaru 58.

"Shugaban ma'aikatan tsaro na sama ya kai shekaru 37 yana aiki, shugaban ma'aikatan tsaro na ruwa yayi shekaru 41.

"Muna so mu tabbatar wa da shugaban kasa, koda baya tunanin saukesu, ya bar su su yi murabus kamar yadda sauran ma'aikata suke yi. Amma kamar yadda doka ta tanadar, zai iya daukansu a matsayin ministan tsaro, masu bayar da shawarwari a kan harkokin tsaro, NSA, da sauransu," yace.

KU KARANTA: Okorocha ga Buhari: Ka fatattaki dukkan masu mukami da hadimanka, sun gaza

A wani labari na daban, Bukola Saraki, shugaban kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP ya ce yakamata shugabanni su dakata da neman kujeru, su hada kan 'yan kasa, a gyara makarantu sannan su janye duk wasu matsalolin da ke raba kawunan al'umma.

Ya shawarci shugabanni masu neman kujerun siyasa, da su dakata na wucin gadi, a gyara kasar nan tukunna. Yakamata su nuna cewa su 'yan kasa nagari ne, Premium Times ta wallafa.

Saraki ya ce, "Duk wata jam'iyya ko kuma dan siyasa wanda bai damu da matsalar da ke addabar kasar nan ba a wannan lokacin, bai cancanci rike wani mukami ba a kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel