Gwamnonin Najeriya 36 zasu gana da Buhari kan lamari saro
Gwamnonin Najeriya 36 sun yanke shawaran ganawa da shugaba Muhammadu Buhari na ba da dadewa ba domin tattauna lamarin tsaro a fadin tarayya, musamman bisa abin da ya faru a Borno.
Gwamnonin sun yanke hakan a zaman kungiyar gwamnonin Najeriya NGF a ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.
Gwamnonin da kungiyar ta aike jihar Borno domin jajantawa gwamna Babagana Umara Zulum ranar 1 ga Disamba sun dawo musu da bayanan abinda suka ganewa idanuwansu a Garin Kwashebe a karamar hukumar Jere ta jihar.
A takardar da kungiyar gwamnonin NGF ta saki a Abuja ranar Juma'a, sun ce zasu goyi bayan duk wani abu da za'ayi domin gyara hukumar yan sanda.
Karin bayani na nan tafe....
Asali: Legit.ng