Gwamnati ta gina tashar wuta mai cin 3.5MW daga hasken rana a FUAM

Gwamnati ta gina tashar wuta mai cin 3.5MW daga hasken rana a FUAM

- Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da aikin wuta a Jami’ar Makurdi

- Daga yanzu Jami’ar za ta rika samun wuta ne daga karfin hasken rana

- FUAM ce Makaranta ta biyu bayan BUK da aka hada wa wannan tasha

Gwamnatin tarayya ta dage wajen ganin an samu wutar lantarki a Najeriya. Wannan ya sa aka fara koma wa karfin hasken rana domin raba kafa.

Jaridar The Nation ta ce a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, 2020, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da wani aiki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnati ta gina wata tasha da za ta rika samar da megawatt 3.5 na karfin wuta daga tsantsar haske da zafin rana.

An kafa na’urorin samar da hasken wuta daga karfin rana ne a jami’ar tarayya ta Makurdi, Benuwai.

KU KARANTA: Sojoji sunyi magana kan zargin 'gazawa' da nemo aron Mayaka

Jami’ar nan ita ce ta biyu da aka jawo mata hasken wuta daga karfin rana, ta na cikin makarantun da gwamnati ta ware domin a haskaka.

Naira biliyan 10 shugaba Muhammadu Buhari ya ware wa wadannan makarantu tara da za su rabu da samun hasken wuta daga lantarki da aka saba.

Hasken wutan rana zai bada dama ga jami’o’in su samu tsayayyen wuta da za su rika yin bincike.

Tashar wutar tana cikin jami’ar a garin Makurdi. A lokacin da ‘yan jarida suka ziyarci makarantar, ana kokarin ganin an kammala tsare-tsaren dake kasa.

Gwamnati ta gina tashar wuta mai cin 3.5MW daga hasken rana a FUAM
Tashar wuta mai cin 3.5MW Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya tashi cikin tsakar dare, ya roki Allah gafara - Sule Lamido

Ana sa ran cewa Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi wajen kaddamarwar bayan ya samu kyakkyawar tarba a jami'ar.

A makon nan ne hukumar EFCC ta bukaci a daga shari’arta da Diezani Alison-Madueke, zzuwa 2021 bayan ta gaza kamo tsohuwar Ministar man ta Najeriya.

Kotu tace Hukumar EFCC ta fito da tsohuwar Minista, Eiezani Alison-Madueke a ranar 3 ga watan Maris, 2021, inda za a cigaba da sauraron karar lauyan EFCC.

Alkali ta sa ranar da EFCC zata kawo mata Diezani Alison-Madueke gaban kotu ne a ranar Laraba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel