Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 12, sun cafke wasu 26 a Katsina

Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 12, sun cafke wasu 26 a Katsina

- Rundunar Operation Sahel Sanity da ke Karamar hukumar Faskari a jihar Katsina suna cigaba da samun nasara

- A cikin 'yan kwanakin nan, rundunar ta samu nasarar kashe fiye da 'yan ta'adda 12, sannan ta mika 26 gaban hukuma

- Mukaddashin darektan yada labarai, Birgediya Bernard Onyeuko ne ya sanar da hakan, inda yace har makamai suka kwace

Rundunar Operation Sahel Sanity wacce take a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, ta kashe fiye da 'yan ta'adda 12, sannan ta damki a kalla wasu 26, a hari daban-daban.

Mukaddashin direktan yada labarai, Bidgediyar Bernard Onyeuko, wanda ya samu wakilcin Kanal Aminu Iliyasu, ya bayyana hakan a wani taro da aka yi a Faskari.

Ya ce rundunar ta samu nasarar kwace bindigogi 11, kirar AK 47, bindigogin toka 3 da shanu 300 a 'yan tsakanin nan, The Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar ya kara bayyana irin nasarorin da aka samu.

Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 12, sun cafke wasu 26 a Katsina
Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 12, sun cafke wasu 26 a Katsina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti

A cewarsa, "A ranar 15 ga watan Nuwamba 2020, yayin da rundunar take sintiri a kauyen Yar Tasha da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, sun ci karo da wasu 'yan ta'adda dauke da miyagun makamai.

"Bayan ganinsu rundunar ta fara ragargazarsu da bindigogi. Sakamakon hakan sun kashe 'yan ta'adda 3, sun kwace bindigogi AK-47 guda 3 da magazines 3 masu rawul 7.62mm na makamai na msuamman. Wasu daga cikin 'yan ta'addan sun tsere da munanan raunuka."

A ranar 16 ga watan Nuwamba 2020, rundunar ta ritsa wasu masu garkuwa da mutane a Garin Arawa da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

KU KARANTA: Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram

Cikin salo da dabara suka lallaba suka hau harbin 'yan ta'addan, sun kashe 1, sauran kuma sun tsere da raunuka. A nan suka samu bindiga AK-47 guda daya, magazine 1 da kuma babur daya.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar ta ragargaji wasu 'yan bindiga a Mararaban Kawaye da kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

A nan take aka kashe 'yan ta'adda 6, aka samu AK-47 guda 4, bindigogin toka 4 da babura 2.

A wani labari na daban, hukumar wani asibiti mai zaman kansa da ke Awka, jihar Anambra ta rike wata Virginia James, mai shekaru 39 a kan kudaden asibiti.

Punch Metro ta gano yadda asibitin ke rike da matar sakamakon yadda ta gaza biyan N248,000 da asibitin suke bin ta bashi.

Matar 'yar asalin Izzi ce, jihar Ebonyi, amma tana zaune a Ifiteisu Awka. Matar ta ce jaririnta ya rasu a asibitin bayan ta fuskanci wahalhalu wurin haihuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng