EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti

EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti

- Wani mutum ya bayyana yadda wani DPO ya kashe mahaifinsa, kawunsa da leburan babansa

- A cewarsa, DPO din da wasu 'yan sanda, sun hada wa mamatan tuggu da makirci sannan suka harbe su

- Don haka ne ya bukaci a hukunta DPO din da sauran 'yan sandan, sannan a biya shi diyyarsu ta naira miliyan 50

Wani Smart Odojie Ofagba, wanda 'yan sanda suka yi sanadiyyar kisan mahaifinsa, Samuel Udojie Ofagba, kawunsa, Abulimen Ofgba da leburan mahaifinsa, Kinsley, yana bukatar gwamnatin tarayya ta biya shi naira miliyan 50.

Ya sanar da wannan bukatar tashi ne yayin sanar da kwamitin bincike a kan wadanda jami'an SARS suka cutar da sauran makamantan laifuka, inda yace wani DPO ne ya kashe masa 'yan uwa a ranar 9 ga watan Maris ta 1999, DPO din shine Aisabor da ke karamar hukumar Usenu Irrua a jihar.

A cewarsa, 'yan sanda sun kama leburan mahaifinsa, bayan ya dawo daga birniya da daddare. Sai suka kai shi wurin mahaifinsa ko zai gane shi, Daily Trust ta tabbatar.

EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti
EndSARS: Yadda DPO ya kashe mahaifina, kawuna da lebura, Matashi ya sanar da kwamiti. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan dankareriyar doya da aka girbe a Anambra wacce ta mamaye mota daya

"Bayan mahaifina ya ga leburan nasa, sai ya tambaye shi abinda ya kawo shi da sassafe, amma sun yi maganar ne da yaren mu. Wani dan sanda ya dakatar dasu, inda yace su yi maganar da turanci don kowa ya gane.

"Sai dan sandan yayi yunkurin marin mahaifina, amma sai yayi gaggawar rike hannunshi, daga nan suka fara sa-in-sa, daga nan suka wuce ofishin 'yan sanda," a cewarsa.

Ya kara da cewa, an sakaya mahaifinsa, kawunsa da leburan babansa a bayan kanta, inda aka bukaci su bayar da N40,000 a matsayin beli. Gaba daya sun tattara tattalin arzikinsu, N23,000, wanda 'yan sandan suka ki amsa.

Smart, wanda a lokacin shekararsa 20, yace 'yan sandan sun bukaci ya koma washegari da safe, tunda dare yayi don ya ga DPO.

KU KARANTA: Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce

"Amma abinda ya bamu mamaki shine yadda muka samu labarin DPO din 'yan sandan ya harbesu, kuma ya kai gawarsu ofishin 'yan sanda na Irrua, inda yace wai 'yan fashi ne."

Ya shirya labarin cewa sun yi harbe-harbe dasu a kan kwanar Ewu, har su na bayyana wata bindigar toka da miyagun makamai, inda suka ce na mahaifina ne da kawuna.

Ya roki kwamitin, inda yace yana bukatar a matsa wa Mr. Aisabor ya nuna masa inda aka birne gawawwakinsu don ya shirya musu birniya wacce ta dace.

Sannan ya bukaci a biya shi diyyar naira miliyan 50, sannan a dauki mataki akan duk 'yan sandan da suke da hannu a kashe-kashen.

Shugaban kwamitin, Ada Ethigiamusoe, ta bukaci a gabatar da Aisabor a gaban kwamitin.

A wani labari na daban, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce a ciki da wajen gwamnati, ya hana Gani Adams, Aaare Ona Kakanfo na kasar yarbawa, kai masa ziyara, The Cable ta wallafa.

OPC, wacce Adams ya jagoranta ta janyo tashin hankali a jihar Legas a lokacin. Bayan nan ne 'yan sanda suka damki Adams, sannan suka rushe OPC.

Ya fadi hakan ne bayan ya ji ana yada cewa sun shirya da Adams bayan rikicin shekaru 15 da suka wuce, Obasanjo ya ce bashi da wata matsala da Adams.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel