Kawai gwadawa nayi, Matashi ya debi amfanin noman da yayi a harabar gidansa

Kawai gwadawa nayi, Matashi ya debi amfanin noman da yayi a harabar gidansa

- Wani matashin dan Najeriya ya gaji da zaman gida sai ya yanke shawaran amfani da lokacin hutu ya shuka doya

- Erhahon ya zabi bayan gidansa domin gwada yin noman lokacin dokar kullen annobar Korona

- Watanni bayan haka, matashin yayi farin cikin girban amfanin gona mai yawa

Osasere Erhahon, matashi dan jihar Edo, yana matukar farin ciki bayan amfanin da ya samu sakamakon noman doyan da yayi a harabar gidansa.

Erhahon ya yanke shawaran shuka doya a gidansa bayan gajiya da zaman gida lokacin dokar kullen cutar Korona; kawai gwadawa yayi a cewarsa.

A labarin da ya wallafa a Facebook, matashin yayi bayanin yadda doyan yayi girma ba tare da ya sa taki ba ko magani.

"Na girbi wannan doyan a bayan gida na mako jiya a Benin. Na yanke shawaran shuka su lokacin dokar kulle ne saboda gajiya da zama, kuma yanzu na samu alheri sosai, " Matashin yace.

"Babu taki, babu magani; kawai haka nayi da shuka. Allah na da girma! Najeriya na da kasa mai albarka."

KU KARANTA: Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano

Kawai gwadawa nayi, Matashi ya debi amfanin noman da yayi a harabar gidansa
Kawai gwadawa nayi, Matashi ya debi amfanin noman da yayi a harabar gidansa
Asali: UGC

KU DUBA: Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus

A bangare, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari kada ya saurari maganan mutane na cire takunkumin hana shigo da shinkafar gwamnati daga kasashen waje.

The Punch ta ruwaito cewa gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ranar Litinin, 30 ga Nuwamba.

Ya yabawa shugaba Buhari kan dokar yayinda ya ambaci muhimman riba biyu da aka ci tun lokacin da aka hana shigo da shinkafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng