Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Malam Ibrahim Shekarau

Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Malam Ibrahim Shekarau

- Bayan lokaci mai tsawo, Sardaunan Kano ya yi tsokaci kan abubuwan dake faruwa a Najeriya

- Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami hafsoshin tsaro

- Ya baiwa Buhari shawara kan abinda zai yi idan ya tubure yana son aiki da su Buratai

Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce shugaban kasan Najeriya na gaba ya zo daga kudancin kasar nan don nuna adalci.

Shekarau ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily.

A cewarsa, duk da cewa ba ya rubuce a kundin tsarin mulkin, "akwai fahimtar daidaito da kuma baiwa kowa daman kama ludayin don adalci."

Yayinda aka tambayeshi kan kiran da yankin Igbo ke yi na a basu shugabancin kasa a 2023, Shekarau yace, "daidaito ne kawai. Ya kamata ayi da kowa."

Ya kara da cewa: "Kundin tsarin mulkin Najeriya ko na jam'iyyar bai ce idan ni dan Arewa ne, wajibi ne mataimaki na ya zo daga kudu ba."

"Ba ya rubuce, amma idan yau na zama dan takaran kujeran shugaban kasa daga Kano, kuma na fada muku mataimaki na dan Bauchi ne, za kuce akwai matsala tattare da ni."

"Arewa tayi shugabancin kasa na shekaru takwas. Aikin hankali shine mu duba dayan bangaren, ya koma kudancin Najeriya."

DUBA NAN: Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe

Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Malam Ibrahim Shekarau
Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Malam Ibrahim Shekarau Credit: @shekarau60
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe

A bangare guda, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na karya doka idan ya cigaba da tuburewa kan kin sallaman hafsoshin tsaron Najeriya.

Sakamakon kisan manoma a Zabarmari na jihar Borno, yan Najeriya sun jaddada kira ga sauke hafsoshin tsaro saboda wadanda ke kai yanzu sun gaza.

Shekarau wanda yayi magana a shirin Sunrise Daily na tashar Channels, ya ce ban da maganan gazawarsu, Sojoji sun zarce shekarun da ya kamata suyi, kuma ana saba doka idan suka cigaba da zama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel