Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a

Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a

- Hausawa su kan ce so tsuntsu ne, yana iya dage fuka-fukansa domin ya canja sheka

- Wata budurwa, wacce suka yi shekaru 2 suna soyayya da wani saurayi ta yanke shawarar canja sheka

- Ta sanar dashi hakan, inda tace lallai ita dai ta samu wanda zai kula da ita, sannan ta yi masa fatan alheri

Wata budurwa mai suna Jumoke ta sha caccaka a kafar sada zumuntar zamani, bayan ta rabu da saurayinta wanda suka yi shekaru 2 suna soyayya.

Kamar yadda wani Sheyi ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, saurayin budurwar, Femi, ya tambayi budurwar dalilinta na daina kula shi daga nan ne ta nuna masa cewa ta canja sheka.

Jumoke ta fara da ce masa ita fa ta gaji da jiransa, tana bukatar more rayuwarta, ta rike masa amanarsa tun lokacin da suka fara soyayya.

Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a
Budurwar da ta bar saurayi talaka saboda mai kudi ta sha caccaka daga jama'a. Hoto daga @Sahmih_Oluboss
Asali: Twitter

Saurayin ya roki budurwar, inda ya bata hakuri yana bukatar ta kara masa lokaci, kafin Ubangiji ya warware masa lamurransa.

KU KARANTA: Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure

Jumoke ta bayyana masa cewa ita fa ba za ta iya jira ba, ta riga ta samu wani wanda zai iya kula da ita. Ta yi wa Femi fatan alheri, daga bisani ta dakatar da shi daga cigaba da yi mata magana.

Bayan wallafa wannan tattaunawa tsakanin saurayi da budurwarsa, mutane da dama sun yi ta cece-kuce.

Wasu suna yin Alla-wadai da yadda Jumoke ta watsar da soyayyarsu ta shekara 2, wasu kuma suka yaba mata inda suka ce babu dalilin da zai sa ta cigaba da jira mara tabbas.

KU KARANTA: Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tanada duk wasu abubuwan da ya kamata ta samu don ta daukaka.

Ya fadi hakan a ranar Talata, lokacin da ya je wata kaddamarwa ta NASIDRC a Lafia, jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Inda yace Najeriya tana da duk wani abu da kasa take bukata, tana da masu fasaha, maza da mata, masu tunani da ma'adanai iri-iri wadanda ake nema don kasa ta daukaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng