Matsalar Tsaron Najeriya ta fi ƙarfin Soja,inji Gwamnati.
- Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) a jiya sun gano cewa matsalolin tsaron Najeriya sun fi ƙarfin sojan Najeriya.
- Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, shine ya bayyana hakan a Maiduguri
- A ranar Laraba ne tawagar NGF ta ziyarci jihar Borno domin jajantawa gwamna Zulum a kan kisan manoma 43
Fayemi ya yi magana lokacin da ƙungiyar gwamnoni ta kai ziyarar ta'aziyya don yin jaje ga gwamnati da mutanen jihar Boorno bisa harin da ƴan Boko Haram su ka kai, wanda ya jawo kisan gillar manoma fiye da 43 a cikin gonakinsu.
Ya ce, "mai girma gwamna, mun zo nan don nuna alhininmu gami da miƙa ta'aziyyar mu ga iyalai da masoyan waɗanda suka rasa rayukansu, da kuma zuwa ga mutanen Borno masu kirki, da kai kanka a matsayinka na shugaban mutanenmu a nan.
"Amma abin da ya faru a kwanaki ukun da suka wuce ya zarce hankali da tunani, ya zarce tsammani, an yi kisan kiyashi kuma yana ɗaya daga cikin kisan da bai zo da sauƙi ba."
Fayemi ya cigaba da cewa "Wannan ba ziyara bace don nuna mun cika aikin mu ba. A'a; ziyara ce don mu nuna fushi bisa gazawarmu saboda mun yi tattaunawa da yawa wanda ka halarta, wasu har da shugaban ƙasa, wasu da shugabannin tsaro.
"Mun tattauna akan dukkan batutuwa, ka yi maganar da ta dace ta gaskiya a dukkan tarukan, amma har yanzu dai muna nan jiya a yau, a inda muke.
"Ba zamu iya dawo da mutanen da aka rasa ba a kwanakin nan da suka gabata, amma idan har ba mu ɗauki ƙwararan matakan da suka dace ba, gabaɗaya ƙasa ce zata faɗa cikin wannan balahirar da tashin hankalin."
Gwamna Fayemi yace ƙungiyar zata cigaba da bawa gwamnatin Maiduguri goyon baya da tallafin da ya kamata don saka hukumomin da suka dace don samo mafita kan matsalolin tsaro.
KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43
"Mu na buƙatar mu tsaya kyam, da kafafu biyu, a bayanka, mu tallafe ka ta kowacce irin hanya da ka buƙata, mu tabbatar gwamnatin mu ta ɗauki matakin da ya dace wajen daƙile wannan matsalar".
"Ina mai tabbatar maka ba zamu yi ƙasa a guiwa ba a matsayin mu na ƴan'uwanka wajen miƙa wannan matsalar wurin hukumomin da ya dace,".
Da yake maida martani, Gwamna Zulum ya koka akan cigaba da kaiwa waɗanda basu ji ba, basu gani ba, hari a jihar.
Ya ce "mu na buƙatar gano bakin zaren abubuwan da suke haddasa tada ƙayar baya, muna yabawa ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen aiwatar da wasu tsare tsare da akayi su don magance talauci a ƙasa baki ɗaya."
"Mun faɗi duk abin da zamu faɗa;ba wani sabon abu da zan iya faɗa. Amma yaushe zamu magance matsalar tsaro da ƴan tada ƙayar baya? Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci."
Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.
A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng