Okorocha ga Buhari: Ka fatattaki dukkan masu mukami da hadimanka, sun gaza
- Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shawarci Buhari da ya fatattaki kaf ministoci da hadimansa
- A cewarsa, maye gurbinsu da masu jini a jika da son hidimta wa kasa ne kawai zai kawo karshen matsalolin nan
- Ya kuma roki daukacin jama'ar Najeriya da su bai wa gwamnati hadin kai don kawo karshen ta'addanci da yunwa
Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, inda ya shawarcesa da ya fatattaki kaf ministoci da hadimansa don sun gaza yin ayyukansu yadda ya kamata, The Nation ta wallafa.
Ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Lafia, lokacin da ya kai gaisuwa ga Gwamna Abdullahi Sule a gidan gwamnati da iyalansa bisa rashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Mr. Philip Tatari Shekwo wanda 'yan bindiga suka kashe.
A cewarsa, "Ya kamata shugaba Buhari ta fatattaki kaf mutanen da ya dauka don su yi wa kasar nan aiki, don sun kasa aiwatar da komai.
KU KARANTA: Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili
"Hakan ne kadai zai taimaka wurin farfado da kasar nan, sannan hakan zai tseratar da Najeriya daga sukar shugabannin kasashen ketare. Kowa a fusace yake a kan al'amarin da ke faruwa a kasar nan."
"Ya kamata a damki duk wadanda suke da hannu a kashe-kashen Borno, jihar Nasarawa da sauran jihohin kasar nan, a kashe su. Ya kamata a kawo karshen kashe-kashe a kasar nan, saboda hakan zubar da kimar Najeriya ne.
"Ya kamata Buhari ya nemi mutane masu jini a jika, wadanda a shirye suke da su yi wa kasa ayyuka, saboda akwai kasashe da dama da suka taba fuskantar kwatankwacin haka kuma ya wuce, har kasar ta farfado ta samu cigaba," a cewar Okorocha.
KU KARANTA: Boye matar aure: Wata kotu a Kano ta bukaci Rarara da ya bayyana a gabanta
Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kara hakuri kuma su bai wa gwamnati hadin kai don kawo karshen rashin aikin yi da yunwar da ke addabar kasar nan.
A wani labari na daban, iyalan wani babban dan kasuwa daga jihar Katsina, Mahdi Shehu, sun bayyana irin hatsarin da rayuwarsa take ciki, a ranar Talata, inda suka ce tun bayan 'yan sanda sun kama shi, ba su sake ji daga shi ba.
Tun bayan Mahdi Shehu, wanda shine shugaban Dialogue Groups, ya zargi gwamnatin jihar Katsina da yin almubazzaranci da naira biliyan 52.6 daga asusun tsaron jihar a shekaru 5 da suka gabata, ya shiga cikin tashin hankali.
Wani daga cikin iyalansa, ya tattauna da Daily Trust a ranar Talata, inda yace ranar karshe da suka ji daga gareshi shine bayan maciji ya sare shi a harabar hedkwatar 'yan sanda dake Area 10 a Garki, Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng