Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki

Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki

- An kammala gyaran tashar rarrabe wutar lantarki da ta samu matsala a ranar Lahadi

- Mukaddashin darekta janar na TCN ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Laraba a Abuja

- Abdulaziz ya ce mintuna 40 kacal suka dauka yayin gyaran don tabbatar da mutane basu cutu ba

TCN ta ce an gyara tashar rarrabe wutar lantarkin da ta samu matsala 'yan kwanakin da suka gabata, jaridar The Punch ta wallafa.

Mukaddashin darekta janar na TCN, Sule Abdulaziz ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Abdulaziz ya ce tun bayan aukuwar lamarin ranar Laraba, mintuna 40 kacal suka dauka kafin su kammala gyaran.

Ya ce kamfanin ya dukufa cikin hanzari wurin gyaran na Abuja, tukunna suka yi na sauran jihohin da abin ya shafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya amince bayyana gaban 'yan majalisa a kan rashin tsaro, Gbajabiamila

Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki
Bayan lalacewar babbar tashan wutan lantarki ta kasa, TCN ta fadi halin da ake ciki. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

A cewarsa, ba wani sabon abu bane a wurinsa, dama hakan yana iya faruwa a ko wacce kasa, kuma a koyaushe.

A cewarsa, "Tun da na hau kujerar nan, ba a taba samun irin wannan matsalar ba, sai ranar Lahadi, kuma bai dauki wani dogon lokaci ba aka gyara."

"Muna cigaba da kulawa da tashar don ba maso kwatankwacin haka ya sake faruwa, amma abinda yafi muhimmanci shine yadda abin ya faru kuma aka yi gaggawar gyarawa.

"A kalla an yi watanni 6 hakan bai faru ba, sai wannan karon," A cewarsa.

Ya kara da cewa, a 'yan watannin nan da yayi a ofishinsa, ya tabbatar ya kara gyara tsarin kamfanin don samun tsayyayar wutar lantarki.

KU KARANTA: Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda

A wani labari na daban, Abdulazeez Abdullahi, shugaban yada labarai na kamfanin rarrabe wutar lantarkin jihar Kaduna, ya tabbatar da aukuwar wani lamari a wata takarda da ya gabatar ranar Lahadi.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Abdullahi ya sanar da lalacewar tashar samar da wutar lantarki ta kasa, da misalin karfe 11:26 na safiyar Lahadi.

Kamar yadda ya wallafa, "Muna masu takaicin sanar muku da za ku fuskanci rashin wutar lantarki a jihar Kaduna, Sokoto, Kebbi da jihar Zamfara, sakamakon lalacewar tashar rarrabe wutar lantarki ta kasa. Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 11:26 na safe."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel