Yanzu-yanzu: An dawo da AbdulRashid Maina Najeriya daga Nijar

Yanzu-yanzu: An dawo da AbdulRashid Maina Najeriya daga Nijar

- Wasa buya ya kare, an dawo da mutumin da ake zargi da almundahana Najeriya bayan ya gudu daga Nijar

- Hukumar yan sanda ta saki hotunan Maina yayinda ya sauka Najeriya

- Alkali ya bada umurnin damkeshi a mayar da shi gidan yari

Hukumar yan sandan Najeriya ta dawo da AbdulRashid Maina, gida bayan guduwar da yayi zuwa kasar Nijar.

Hukumar ta bayyana hakan ne da ranar nan a shafinta na Tuwita.

Tace: "Hukumar yan sanda ta dawo da AbdulRashid Abdullahi Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran aikin fansho, yau, 3 ga Disamba, 2020 daga Niamey, jamhurriyar Nijar."

"An shigo da tsohon shugaban fanshon Najeriya cikin jirgin yan sanda mai lamba 5N-HAR kuma ya sauka daidai karfe 14:17 na ranar."

Yanzu-yanzu: An dawo da AbdulRashid Maina Najeriya daga Nijar
Yanzu-yanzu: An dawo da AbdulRashid Maina Najeriya daga Nijar Credit: @PoliceNG
Source: Twitter

KU KARANTA: Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Malam Ibrahim Shekarau

KU DUBA: Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi

A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya baiwa Maina kuma ya bada umurnin daureshi.

Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kurkuku maimakonsa ko ya biya kudi N500m.

Bayan kwana hudu da tsare Ndume, Alkali Abang ya bada belin Sanatan.

Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma'a ya ce ya baiwa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na halayya mai kyau, amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel