Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi

Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi

- Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kayan tallafi ga al'ummar jihar Borno

- Wannan tallafi na zuwa ne yan kwanaki bayan harin da aka kaiwa manoma a jihar

- Ministar walwala da agaji ta jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin kai kayan

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin raba kayan tallafi ga iyalan da kisan manoma 44 da yan ta'addan Boko Haram suka hallaka a jihar Borno.

Ministar tallafi da jin dadin jama'a, Sadiya Farouk, ta wanzar da umurnin ranar Laraba, 2 ga Disamba, 2020.

Hajiya Farouk ta ziyarci jihar Borno ne tare da abokan aikinta da takwararta, Ministar harkokin mata, Dame Pauline Tallen, da shugaban hukumar cigaban arewa maso gabas, Mohammed Goni.

Gabanin garzayawa kauyen Zabarmari a karamar hukumar Jere domin haduwa da iyalan mamata, ministar ta kaiwa gwamnan jihar Babagana Zulum gaisuwar ta'aziyya.

Tace: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin harin kuma ya umurceni in kawo kayan tallafi daga gwamnatin tarayya ga iyalan mamatan da wadanda abin ya shafa."

Kayan da aka rabamusu sun hada da: Buhun shinkafan 12.5kg 13,000; buhun masara 12.5kg 13,000; buhun wake 25kg 13,000; galolin man gyada 1,300; kwalayen dandano 2,116; kwalayen tumatur na gwangwani 1,083; da jakunan gishiri 650.

KU DUBA: Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau

KU KARANTA: Lauyan Maina ya yi watsi da shi, ya janye daga kareshi a kotu

Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi
Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi CREDIT: @FMHDSD
Source: Twitter

Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi
Gwamnatin tarayya ta kaiwa iyalan manoman da aka kashe a Borno tirelan hatsi CREDIT: @FMHDSD
Source: Twitter

A bangare guda, Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya na cikin wadanda suka mike a majalisar dattawa, suka koka game da sha’anin tsaro a makon nan.

Sanata Kashim Shettima ya yi Allah-wadai da kisan manoma 67 da ake zargin an yi a garin Zabarmari. Shettima ya ce garin bai da nisa da Maiduguri.

A cewar Kashim Shettima, abin da ya faru a kauyen Zabarmari, yana cikin mafi munin hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi tun da suka fara ta’adi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel