Da duminsa: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda

Da duminsa: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda

- Za'a dawo da AbdulRashid Maina gida bayan damkeshi a kasar Nijar

- Maina ya gudu daga Najeriya bayan kotu ta bashi beli

- Maina bayan guduwansa ya ce jinya karayar da ya samu a kafa yakeyi shi yasa bai zuwa kotu

Hukumar yan sandan Najeriya ta fara shirye-shiryen dawo da tsohon shugaban kwamitin gyaran hukumar fanshi, AbdulRashid Maina, wanda aka damke a birnin Niamey, jamhuriyyar Nija, ranar Litinin.

Hadakar hukumar yan sandan Najeriya da na INTERPOL sun damkeshi ne bayan guduwa da yayi daga Najeriya.

Yanzu haka yana tsare a hannun hukumomin Nijar kafin a dawo da shi.

Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, Frank Mba, a jawabin da ya saki ranar Talata yace hukumar na kokarin ganin an dawo dashi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP

Hukumar yan sanda a jawabi mai take, 'Za'a dawo da Abdulrashid Maina nan ba da dadewa ba,' yace, "Sakamakon damke tsohon shugaban hukumar gyaran harkan fansho AbdulRashid Maina a Niamey, jamhuriyyar Nijar, hukumar yan sandan Najeriya na kokarin dawo da shi Najeriya domin gurfanar da shi a kotu kan zarge-zargen da ake masa."

"An damke Maina, wanda aka alanta nemansa ruwa a jallo, ranar 30 ga Nuwamba, 2020 ta hanyar hadin kai tsakanin jami'an yan sandan Najeriya, INTERPOL da yan sanda Nijar."

Da duminsa: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda
Da duminsa: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan manoma 73 a Zabarmari: Sheikh Ahmad Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako

A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya baiwa Maina kuma ya bada umurnin daureshi.

Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kurkuku maimakonsa ko ya biya kudi N500m.

Bayan kwana hudu da tsare Ndume, Alkali Abang ya bada belin Sanatan.

Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma'a ya ce ya baiwa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na halayya mai kyau, amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel