Dalilin da yasa na yi wa Shugaba Buhari takwara da tagwayen da na haifa, Gwamna Sule
- Gwamnan jihar Nasarawa ya rada wa tagwayensa sunan shugaba Muhammadu Buhari da na Umar Al-Makura
- Ya ce ya rada wa yaransa sunayensu ne saboda darajawa da mutuntawa da ke tsakaninsa da shugabannin biyu
- Manyan masu fadi a ji, kamar mataimakin gwamnan jihar, kakakin majalisar jihar da sauransu sun halarci taron
Gwamnan jihar Nasarawa ya rada wa tagwayensa sunan Shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Bayan amaryar gwamnan, Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta haifi zankada-zankadan ragwayenta, an yi shagalin sunan a ranar Talata a cikin fadar sarkin Gudu a karamar hukumar Akwanga, Alhaji Sule Bawa, wanda shine mahaifin gwamnan.
Gwamnan ya ce: "Na radawa yarana sunayen shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura saboda girmamawa ta a garesu.
"Na yi alkawarin cigaba da samar da ilimi mai inganci ga daukacin yaran jihar Nasarawa."
KU KARANTA: Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo)
Sarkin Lafiya, Justice Sidi Bage, ya bayyana tagwayen a matsayin albarka kuma ya yi musu fatan samun lafiya mai daurewa sannan da fatan za su zama 'yan kasa na gari.
Babban limamin Gudi, Malam Mohammad Awal Musa Dandaura, shi yayi radin sunan sannan yayi wa yaran addu'o'i, shugabanni, jihar da Najeriya bakidaya.
Taron da ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, Dr Emmanuel Akebe, Sanata Abdullahi Adamu da kakakin majalisar jihar, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi, da sauran manyan mutane.
KU KARANTA: Kisan manoma 73 a Zabarmari: Sheikh Ahmad Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako
A wani labari na daban, iyalan wani babban dan kasuwa daga jihar Katsina, Mahdi Shehu, sun bayyana irin hatsarin da rayuwarsa take ciki, a ranar Talata, inda suka ce tun bayan 'yan sanda sun kama shi, ba su sake ji daga shi ba.
Tun bayan Mahdi Shehu, wanda shine shugaban Dialogue Groups, ya zargi gwamnatin jihar Katsina da yin almubazzaranci da naira biliyan 52.6 daga asusun tsaron jihar a shekaru 5 da suka gabata, ya shiga cikin tashin hankali.
Wani daga cikin iyalansa, ya tattauna da Daily Trust a ranar Talata, inda yace ranar karshe da suka ji daga gareshi shine bayan maciji ya sare shi a harabar hedkwatar 'yan sanda dake Area 10 a Garki, Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng