Budurwa ta kashe saurayinta bayan ya bukaci ta harbeshi don gwada maganin bindiga
- Matashi ya bukaci budurwarsa ta harbeshi da bindiga domin gwada sihhancin maganin bindigan da ya sha
- Matashin wanda akafi sani da 'Email' ya mutu har lahira bayan harbin da tayi masa
Wani matashi ya rasa ransa a garin Calabar yayinda ya bukaci budurwarsa ta harbeshi da bindiga domin gwada sihhancin maganin bindigan da ya sha.
Matashin wanda akafi sani da 'Email' ya mutu har lahira bayan harbin da tayi masa.
Vanguard ta ruwaito cewa mamacin ya kasance dan kungiyar daba kuma mai sayar da kwayoyi na tare da abokansa ne lokacin da abin ya faru a gidansa dake Nelson Mandela street, Calabar South.
Wata majiya ta bayyana cewa tsautsayin ya faru ne misalin karfe 11 na safe inda matashin da abokansa suka sha maganin da aka basu da sunan na bindiga da harsashi.
Majiyar tace: "Sauran sun gwada kuma tayi aiki amma matashin ya zabi budurwarsa ta harbeshi domin tabbatar da sihhancin maganin a jikinsa, amma kash harbin da tayi masa ya ratsa jikinsa kuma ya mutu nan take,"
Wasu daga cikin abokan matashin suka fusata inda suka yi takan yarinyar da adduna suna saranta kafin aka kira yan sanda.
Bincike ya nuna cewa yan sanda sun dauki gawar matashin kuma an kai yarinyar asibiti don jinya.
Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan Cross River, DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwan lamarin kuma ta tabbatar da cewa yarinyar na asibitin yan sanda.
KU KARANTA: Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana
KU DUBA: Okorocha ga Buhari: Ka fatattaki dukkan masu mukami da hadimanka, sun gaza
Kotun Majistare ta IV a Birnin Kebbi, ta bada umurnin garkame wata mata mai suna, Patricia Nebochi, a gidan yarin Argungun kan laifin satan dan jariri a jihar.
Matar, mai zama a garin Tambuwal ta saci jaririn ne a asibiti Aisha Muhammadu Buhari dake garin Jega, Daily Trust ta ruwaito.
Miss Nebochi, ta saci yaron wata mata mai suna Fatimah Galbi, yar garin Galbi, karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng