'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya

'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya

- Wasu 'yan ta'adda da ake zargin cewa 'yan fashi da makami ne sun hallaka mataimakin kwamsihinan 'yan sanda, Egbe Edum

- Edum, mai mukamin kwamishinan 'yan sanda, ya gamu da ajalinsa a hanyarsa ta zuwa gida domin ganin iyalinsa

- 'Yan ta'adda sun kai farmaki kan Edum yayin da ya ke tafiya a gefen wata babbar hanya bayan motarsa ta lalace da tsakar dare

Wasu miyagun 'yan ta'adda, da har ya zuwa yanzu ba'a tantance su waye ba, sun kashe babban jami'in dan sanda a yankin kudu maso kudu.

Dan sandan, Egbe Edum, mai mukamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, ya gamu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalinsa a jihar Kuros Riba.

'Yan ta'addar sun kai wa Edum hari da safiyar ranar Laraba a yankin garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba.

KARANTA: An tsayar da ranakun rubuta jarrabawoyin daukan aiki a NIS da NSCDC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta tabbatarwa da jaridar Premium Times faruwar lamarin.

'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya
'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya @Thecable
Source: Twitter

"Duk da har yanzu mu na kan gudanar da bincike, takaitaccen bayanin da ke hannunmu ya nuna cewa ya zo gari ne daga Maiduguri domin ziyarar iyalinsa. Shi dan asalin nan ne.

"Ya iso nan da misalin karfe 1:00 na dare, amma sai motarsa ta samu matsala a kan hanya, har ma ya Kira matarsa domin ta zo ta dauke shi.

"Ya na cikin tafiya da kafa a gefen hanya ne sai wasu miyagun batagari su ka far masa da sara da suka," a cewar Ugbo.

KARANTA: Zaben LGAs: Ra'ayin Kwankwasiyya ne ba na jam'iyya ba, PDP ta dare gida biyu a Kano

Kakakin ta bayyana cewa ana zargin 'yan fashi ne suka kai wa Edum hari.

Wata jaridar jihar Kuros Riba da ke wallafa labaranta a yanar gizo, CrossRiverWatch, ta wallafa labarin dauke da hoton motar Edum kaca-kaca da jini a gefen wata babbar hanya da ke Calabar.

Takardun motar sun tabbatar da cewa marigayi Edum ne ya mallake ta.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa DPO na ofishin rundunar 'yan sanda da ke Otukpo a Makurdi, SP Yahaya Pawa, ya tsallake rijiya da baya.

Wasu batagarin 'yan ta'adda sun dirkawa SP Pawa dalma a yayin da ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa kamen ma su laifi a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

SP Pawa da jami'an tawagarsa sun yi dirar mikiya a kan batagarin a daidai lokacin da su ka baje kolin kayan da suka sato daga shagunan 'yan kasuwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel