Batagari sun harbi DPO Yahawa Pawa yayin da ya jagoranci samamen kamen ma su laifi
- DPO na ofishin rundunar 'yan sanda da ke Otukpo a Makurdi, SP Yahaya Pawa, ya tsallake rijiya da baya
- Wasu batagarin 'yan ta'adda sun dirkawa SP Pawa dalma a yayin da ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa kamen ma su laifi
- SP Pawa da jami'an tawagarsa sun yi dirar mikiya a kan batagarin a daidai lokacin da su ka baje kolin kayan da suka sato
Wasu ɓatagari sun harbi DPO ofishin ƴan sanda da ke Otukpo, SP Yahaya Pawa da safiyar ranar Talata a unguwar Otukpo da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa DPO Pawa ya jagoranci tawagar jami'an ƴan sandan don su ƙwamuso wasu masu laifi da ake zargin sun fake a yankin da lamarin ya afku.
An gano cewa masu laifin suna da hannu dumu dumu a satar kayayyakin da akayi a kasuwar Otukpo lokacin da gobara ta tashi a makon dsa ya gabata.
Su na tsakiyar cin kasuwar kayan satar ne, sai tawagar ƴansanda a ƙarƙashin DPO Pawa suka bayyana a wurin da suke kasuwancin.
KARANTA: Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aikin Lakcarin a matakin Farfesa
Ɓatagarin dai sun yi bajakolin kayayyakin da suka sato daga kantinan ƴan kasuwa, wanda suka haɗar da kayan sawa da sauran kayan amfanin gida, a wajen garin Otukpo kamar yadda labari ya samu rundunar ƴan sanda.
Ƴan sanda na tsaka da cafke masu laifin sai wasu daga cikinsu suka ɗirkawa DPO alburushi, sannan suka cika bujensu da iska.
KARANTA: Saukaka Sufuri: Buhari ya bayar da umarnin sakin manyan motocin jigilar mutane
Da aka tuntuɓe ta, Kakakin rundunar ƴansandan jihar Benue, Catherine Anene, ta tabbatar wa da ƴan jarida faruwar lamarin a Makurdi.
Anene ta ce"Da gaske ne wasu ɓatagari sun harbi DPO lokacin da ya jagoranci tawagarsa Atisaye."
"Amma DPO yana nan da ransa cikin ƙoshin lafiya, sun harbe shi ne a kafaɗa."
Daga jihar Nasarawa mai makwabtaka da Benuwe, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jami'an 'yan sanda sun kama kasurgumin dan ta'addan da ya kashe shugaban jam'iyyar APC, Philiph Tatari Schekwo.
Gwamnan jihar Nasara, Abdullahi Sule, shine ya sanar da cewa jami'an 'yan sanda sun cafke mai laifin a Lafia, babban birnin jiha.
A karshen watan Nuwamba ne rahotannin suka bayyana yadda aka je har gida aka kashe mista Schekwo tare da jefar da gawarsa a wani wuri nesa da gidansa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng