An tsayar da ranakun rubuta jarrabawar daukar aiki NIS da NSCDC

An tsayar da ranakun rubuta jarrabawar daukar aiki NIS da NSCDC

- Ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar da cewa za ta gudanar da jarrabaw daukan aiki a hukumominta guda biyu

- Wadanda suka nemi guraben aiki a karkashin hukumomin sun dade suna jiran sanarwar lokacin rubuta jarrabawar

- Ogbeni Rauf Aregbesola, ministan ma'aikatar harkokin gida ya dauki alkawarin cewa za'a tabbatar da adalci da daidaito wajen daukar sabbin ma'aikatan

Gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, ta sanar da cewa ta tsayar da ranakun 7 da 8 ga watan Disamba a matsayin ranakun rubuta jarrabawar daukan aiki a hukumar kula da shige da fice (NIS) da rundunar tsaro ta NCSDC (Nigerian Security and Civil Defence Corps).

Fiye da 'yan Najerya miliyan biyu ne suka nuna sha'awar samun gurbin aiki a hukumomin guda biyu da ke karkashin ma'aikatar harkokin cikin gida.

A cikin wani jawabi da Alhaji Mohammed Manga, darektan yada labarai a ma'aikatar harkokin cikin gida, ya fitar, ya ce ma'aikatarsu ta hada kai da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) wajen gudanar da jarrabawoyin.

KARANTA: Saukaka Sufuri: Buhari ya bayar da umarnin sakin manyan motocin jigilar mutane

An tsayar da ranakun rubuta jarrabawar daukar aiki NIS da NSCDC
An tsayar da ranakun rubuta jarrabawar daukar aiki NIS da NSCDC @Rauf Aregbesola
Asali: Facebook

Alhaji Manga ya bayyana cewa za'a gudanar da jarrabawar ta hanyar amfani da tsarin amsa tambayoyi a na'ura mai kwakwalwa (Computer-Based Test; CBT) domin tabbatar da adalci da dakile magudi da alfarma.

KARANTA: Garba Shehu: An yi min mummunar fassara, ba'a fahimci kalamaina a kan kisan manoma ba

Ya ce sun hada gwuiwa da hukumar JAMB ne domin bayar da dama ga dukkan wadanda suka nemi guraben aiki a hukumomin biyu.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya sanar da cewa ma'aikatarsa za ta tabbatar da adalci da daidaito wajen daukar sabbin ma'aikatan.

A wani labarin daban da Legit.ng ta walafa, wasu ɓatagari sun harbi DPO ofishin ƴan sanda da ke Otukpo, SP Yahaya Pawa da safiyar ranar Talata a unguwar Otukpo da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa DPO Pawa ya jagoranci tawagar jami'an ƴan sandan don su ƙwamuso wasu masu laifi da ake zargin sun fake a yankin da lamarin ya afku.

An gano cewa masu laifin suna da hannu dumu dumu a satar kayayyakin da akayi a kasuwar Otukpo lokacin da gobara ta tashi a makon dsa ya gabata.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng