Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta

Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta

- Jam'iyyar PDP mai hamayyya ta rabu gida biyu a jihar Kano a yayin da zaben kananan hukumomi ke karatowa

- Hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta tsayar da ranar 16 ga watan Janairu a matsayin ranar zaben kananan hukumomi

- A ranar Talata ne tsagin Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP ya sanar da cewa ba za su shiga a fafata da su a zaben ba

Mambobin jam'iyyar PDP ma su biyayya ga Ambasada Aminu a Kano sun nesanta kansu daga sanarwar janyewa daga shiga zaben kananan hukumomi da za'a yi a jihar a cikin watan Janairu na shekarar 2021.

A ranar Talata ne shugaban riko na PDP a Kano, Dakta Danladi Abdulhameed, ya sanar da cewa jam'iyyar ba za ta shiga zaben kananan hukumomin da za'a yi ranar 16 ga watan Janairu ba saboda rashin yarda da hukumar zabe ta jihar Kano.

KARANTA: Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aikin Lakcarin a matakin Farfesa

Sai dai, dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Dala a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Mustapha Mai Royal, ya sanar da Daily Trust, yayin hirarsu ta waya, cewa Dakta Abdulhameed kakakin darikar Kwankwasiyya ne ba na PDP ba.

Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta
Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta @Daily_trust
Asali: Twitter

"Kakakin tafiyar Kwankwasiyya ne ba na jam'iyyar PDP ba. Ambasada Aminu Bashir Wali ne jagoran jam'iyyar PDP a Kano," a cewar Mai Royal yayin da ya ke magana a kan sanarwar janyewa daga shiga zaben.

KARANTA: Saukaka Sufuri: Buhari ya bayar da umarnin sakin manyan motocin jigilar mutane

"Jam'iyyar PDP ba kungiyar Kwankwasiyya ba ce, a saboda haka a shirye mu ke mu shiga zaben da za'a yi ranar 16 ga watan Janairu. Ina magana ne da yawun Aminu Wali. Mun yi magana da shi bayan fitar waccan sanarwa kuma ya umarci mu sanar da mambobinmu su shiga zaben," a cewarsa.

A cewar Mai Royal, tsagin Aminu Wali na jam'iyyar PDP na da 'yan takara a dukkan kananan hukumomin Kano 44 kuma za su mika takardunsu na takara ga hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC).

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, an dawo da wani tsohon bidiyo da shugaba Buhari ke zargin gwamnatin tarayya da zama babbar mai daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke takara, gabanin zaben shekarar 2015.

Dawo da bidiyon tamkar tuni ne ga shugaba Buhari domin ya tuna alakwuran da ya daukarwa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel