Maradona ya bayyana wasu shawarwari da ya bawa Messi da yasa ya zama fitaccen dan kwallo a duniya

Maradona ya bayyana wasu shawarwari da ya bawa Messi da yasa ya zama fitaccen dan kwallo a duniya

- Tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina, Diego Maradona ya bayyana yadda ya raini dan wasa Lionel Messi

- Haka kuma Maradona ya bayyana wasu shawarwari da ya dinga bawa dan wasan a lokacin da ya shugabanci kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina

- Ya ce shine ya raini Messi dan haka babu wanda ya san shi a duniya fiye dashi, shine ya koya masa duka abubuwan da yake yi a yanzu

Fitaccen dan wasan kwallon nan na duniya da tauraruwarsa ta haska a shekarun baya, Diego Maradona, ya bayyana cewa shawarwarin da ya bawa Lionel Messi ne lokacin da yake jagorantar kungiyar kwallon kafa ta Argentina ta saka ya zama fitaccen dan kwallo a duniya.

A cewar Maradona wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai, ya ce irin shawarwari da karfin guiwar da ya dinga bawa dan wasan lokacin suna tare sune suka saka ya zama abinda ya zama a wannan lokacin.

"Ni na koyar da Messi, saboda haka babu wanda ya isa ya ce mini wani abu, saboda yanzu haka ya kere manyan 'yan wasa guda biyar," in ji tsohon dan wasan Barcelonan.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kashe daliban jami'a guda biyu, bayan sun kaiwa matar gwamnan APC hari

"Yana da matsala wajen buga 'free-kicks', duk lokacin da muka kammala wasa ina dakatar da Messi domin na kara koya masa.

"Ban koya masa yadda ake buga 'free-kick' ba, sai ya tambayeni ya aka yi nake iya cin kwallo, na bashi amsa cewa kawai ya buga ta tsakiya.

"Sai ya bani amsa da cewa ai ya buga tsakiyar kuma sai yaga ta baude, sai nace kada ya damu ya cigaba da bugawa watarana zai yi nasara, yanzu gashi baya zubarwa idan ya samu," in ji tsohon dan wasan kwallon kafar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel