Da duminsa: An kama 'yan ta'addan da suka kashe shugaban APC na jihar Nasarawa

Da duminsa: An kama 'yan ta'addan da suka kashe shugaban APC na jihar Nasarawa

- A ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, aka wayi gari da samun labarin yin garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philiph Schekwo

- Jim kadan bayan samun labarin sace shi, sai ga shi rahotanni sun sanar da cewa an tsinci gawarsa

- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, ya sanar da cewa an kama dan ta'addar da ya kashe Schekwo har gida

An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya kashe Cif Philip Tatari Shekwo, shugaban jam'iyyar APC a jihar Nasarawa, kimanin sati biyu da suka gabata.

A ranar Talata ne Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da cewa 'yan sanda sun kama dan ta'addan a garin Lafia, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

A cewar gwamna Sule, an kama dan ta'addar mai suna Mohammed Usman a Asakio, karamar hukumar Lafia ta gabas, kuma tuni ya amsa laifinsa a hannun rundunar 'yan sanda.

KARANTA: Wata Jami'ar kasar Amurka ta bawa Ganduje aikin koyarwa a matsayin Farfesa

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun zo gidan marigayi Schekwo da ke kan titin Kurikyo kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a garin Lafia da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare 11pm inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Da duminsa: An kama 'yan ta'addan da suka kashe shugaban APC na jihar Nasarawa
Da duminsa: An kama 'yan ta'addan da suka kashe shugaban APC na jihar Nasarawa @Vanguard
Asali: Twitter

Ƙarar harbin bindigun ne suka tashi marigayi Schekwo daga barci, inda nan take ya gano cewa akwai matsala, kuma take ya fara kiran lambobin wayar hukumomin tsaro amma basu ɗaga ba har aka ƙwamushe shi.

KARANTA: A karshe: An gama wasan buya, an kama Abdulrasheed Maina a Nijar

A daya daga cikin rahotannin da ta wallafa a kan kisan marigayi Schekwo, Legit.ng Hausa ta rawaito Mr Joseph Gudu, maƙwabcin marigayin, ya ce akan idonsa komai ya faru domin kuwa yana hango komai ta tagar gidansa.

Ya bayyana yadda ƴan bindigar suka yi amfani da garma wajen karya ƙofar gidan da tagogin gidan.

A cewar Gudu, marigayi Schekwo ya yi kira tare da ihun neman taimako amma duk a banza, babu wanda ya kawo masa agaji har 'yan ta'adda suka cimmasa bayan kusan sa'a guda.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel