A karo na biyu cikin rana guda: Sojoji sun sheƙe ƴan bindiga 5 tare da kuɓutar da mutane 9 daga hannunsu a Kaduna

A karo na biyu cikin rana guda: Sojoji sun sheƙe ƴan bindiga 5 tare da kuɓutar da mutane 9 daga hannunsu a Kaduna

- 'Yan bindiga sun matsa wajen yawaita kai hare-hare a yankin Zaria da kewaye a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon daren ranar Lahadi ana barin wuta a tsakanin sojoji da 'yan bindiga a tsakanin Zaria zuwa Kaduna

- Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Kaduna, ya ce wasu mutane biyar da aka kubutar sun ce 'yan bindiga sun kone gawarwakin 'yan uwansu

Sojojin Najeriya na Atisayen Kwarankwatsa (Operation Thunder Strike; OPTS) sun sheƙe ƴan bindiga biyar a kusa da unguwar Anaba dake ƙaramar Hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar ranar Talata.

Ya ƙara da cewa sojojin sun yi nasarar ceto mutum tara waɗanda aka yi garkuwa da su a wani atisayen na daban.

"Bayanan atisayen soji da aka kawowa gwamnatin jihar Kaduna ranar Talata na nuni da cewa sojoji sun ceto mutane tara ƴan asalin jihar da aka yi garkuwa da su a wurare daban daban.

KARANTA: An kama Mohammed Usman, kasurgumin dan ta'addan da ya kashe shugaban APC na jihar Nasarawa

"Ƴan bindiga da dama sun tsere da raunukan harsasai cikin dajin Malum a cigaba da kai farmakin da ake yiwa ƴan bindigar da suka tare Kwanar Tsintsiya, ƙaramar Hukumar Igabi, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ƙarshen mako."

A karo na biyu cikin rana guda: Sojojin sun sheƙe ƴan bindiga 5 tare da kuɓutar da mutane 9 daga hannunsu a Kaduna
Sojojin sun sheƙe ƴan bindiga 5 tare da kuɓutar da mutane 9 daga hannunsu a Kaduna @Daily_nigerian
Asali: Twitter

"Biyar daga cikin waɗanda aka ceto da safiyar ranar Talata, lokacin da suke bada bayanai, sun bayyana yadda ƴan bindigar suka ƙona gawarwakin ƴan uwansu huɗu," a cewarsa.

KARANTA: Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aikin Lakcarin a matsayin Farfesa

Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni suka miƙa mutane taran 9 da aka kuɓutar gun iyalansu.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa dakarun rundunar soji sun kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Onitsha daga jihar Sokoto, kamar yadda Leadership ta rawaito.

A cikin wani jawabi da kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kadina, Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce dakarun soji sun fafata da 'yan bindigar tun daga daren ranar Lahadi har zuwa awannin duku-dukun safiyar Litinin.

Wani maƙwabcin yankin ya ce tun a daren Lahadi, ƴan bindigar suka tare hanyar tsakanin Jaji da kwanar Faraƙwai, kana suka tare hanyar da ke tsakanin Lamban Zango da Dumbi-Dutse.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel