An kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

An kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

- 'Yan bindiga sun matsa wajen yawaita kai hare-hare a yankin Zaria da kewaye a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon dare ana barin wuta a tsakanin sojoji da 'yan bindiga a tsakanin Zaria zuwa Kaduna

- Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Kaduna, ya ce sojoji sun kubutar da mutane da shanun da 'yan bindigar suka sace

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa dakarun rundunar soji sun kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Onitsha daga jihar Sokoto, kamar yadda Leadership ta rawaito.

A cikin wani jawabi da kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kadina, Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce dakarun soji sun fafata da 'yan bindigar tun daga daren ranar Lahadi har zuwa awannin duku-dukun safiyar Litinin.

Jawabin ya kara da cewa; "dakarun rundunar soji na bataliya ta 4 sun fafata da 'yan bindiga a Kwanar Tsintsiya da ke yankin karamar hukumar Igabi a kan tsakanin Kaduna zuwa Zaria."

KARANTA: Garba Shehu: An yi min mummunar fassara, ba'a fahimci kalamaina a kan kisan manoma ba

Aruwan ya ce 'yan bindigar sun tare hanya tare da budewa matafiya wuta.

An kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
An kubutar da matafiya 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna @Nigerian Army
Asali: Facebook

Kazalika, ya bayyana cewa sojoji sun mayar da martani tare da samun nasarar kashe guda daga cikin 'yan bindigar, yayin da sauran suka gudu da raunukan harbin bindiga.

KARANTA: Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari kan yadda FG ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki

"Bayan isar sojoji zuwa wurin, sun kubutar da mutanen da aka sace da kuma shanu 69 tare da hallaka daya daga cikin 'yan bindigar," a cewar Aruwan.

Legit.ng Hausa da sauran wasu kafafen yada labarai, a ranar Litinin, sun rawaito cewa an shafe tsawon dare guda ana gumurzu tsakani jami'an sojoji da ƴan bindiga akan titin Zaria zuwa Kaduna.

Wani maƙwabcin yankin ya ce tun a daren Lahadi, ƴan bindigar suka tare hanyar tsakanin Jaji da kwanar Faraƙwai, kana suka tare hanyar da ke tsakanin Lamban Zango da Dumbi-Dutse.

Duk da a Aruwan bai bayar da cikakken bayani ba a ranar Litinin, wasu majiyoyi na cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng