Ruf-da-ciki a kan tallafin Korona: An dakatar da wasu ma su Sarauta a Kano

Ruf-da-ciki a kan tallafin Korona: An dakatar da wasu ma su Sarauta a Kano

- Masarautar Rano a jihar Kano ta sanar da cewa ta dakatar da wasu Dagatai guda biyu bisa zargin waskewa da kayan tallafin Korona

- Talakawa da yawa a fadn Nigeria sun yi korafin cewa basu samu tallafin komai ba duk da irin kayan abinci da gwamnati ta aika jihohi

- Ana zargin wasu shugabanni da jagororin jama'a da karkatar da kayan tallafin zuwa kasuwa ko gidajensu

Masarautar Rano ta jihar Kano ta dakatar da wasu Dagatai bisa zarginsu da kane - kane da ruf da ciki akan tallafin COVID-19 da gwamnatin Kano ta bayar a rabawa talakawa don su rage raɗaɗi.

Dagatan da aka dakatar sune Dagacin garin Zambur wato Kamilu Zambur da kuma takwaransa na garin Zurgu, Umar Yusuf.

Sarkin Rano, Alhaji Kabir Muhammadu Inuwa, shine ya bada umarnin a dakatar da Dagatan biyu ta hannun Chiroma kuma Hakimin Rano, Manniru Ila.

KARANTA: Saukaka Sufuri: Buhari ya bayar da umarnin sakin manyan motocin jigilar mutane

Tuni masarautar ta tura wakilan da zasu maye gurbin Dagatan da aka dakatar a garuruwansu.

Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da suka rabauta da tallafin Korona, sai dai akwai masu hana ruwa gudu da suka sauya akalar kayayyakin tallafin zuwa gidajensu da kasuwanni.

Ruf-da-ciki a kan tallafin Korona: An dakatar da wasu ma su Sarauta a Kano
Ruf-da-ciki a kan tallafin Korona: An dakatar da wasu ma su Sarauta a Kano
Source: Facebook

Duk da hakan hukumomi a jihar Kano ba su yi ƙasa a guiwa ba wajen gano masu ƙwamushe kayayyakin tare da cafke su don girbar abinda suka shuka.

KARANTA: A karshe: Wasan buya ya kare, an kama Abdulrasheed Maina a Nijar

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Jami'ar 'East Carolina' da ke kasar Amurka ta aikowa gwamna Ganduje takardar daukansa aikin Lakcari a matsayin Farfesa.

Jami'ar ta ce iliminn Ganduje, kwarewa a mulki, da shaidar kirki da aka yi masa sune silar daukansa aikin

A cikin takardar daukan aiki da ta turo ma sa, Jami'ar ta ce idan har Ganduje ya amince da bukatar Jami'ar, zai shiga sahun manyan malamanta da ke aiki a cibiyar ECU-ICITD.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel