Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari

Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari

- NAS ta bukaci shugaban kasa Buhari da ya sauke shugabannin tsaro kuma ya maye gurbinsu da sabbabi masu jini a jika

- Sannan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta nemi taimakon kawayenta da ke kasashen ketare don kawo karshen rashin tsaro

- A cewar NAS, shugabannin tsaro sun gaza wurin kula da rayuka da dukiyoyin al'umma musamman a arewacin Najeriya

NAS ta bukaci shugaban kasa da yayi gaggawar sauke shugabannin tsaro a kan kashe manoman shinkafa 43 da 'yan Boko Haram suka yi a Zabarmari, a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, jaridar Vanguard ta wallafa.

Mr. Abiola Owoaje, wani jagaban NAS, ya gabatar da wata takarda mai taken "Kisan da 'yan ta'adda suka yi na manoman shinkafan Zabarmari guda 43", ya bayyana al'amarin a matsayin abu mai razanarwa da tsoratarwa.

A cewarsa, "Wannan kisan a cikin kashe-kashen da aka yi ta yi marasa iyaka musamman a arewa maso gabas da sauran yankuna a Najeriya, yana nuna mummunan tsarin harkar tsaron Najeriya tun daga farko."

KU KARANTA: Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari

Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari
Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

"Al'amarin sai karuwa yake yi, ya zama ruwan dare, babu ranar da abin zai kare, 'yan Boko Haram suna cin karensu babu babbaka."

A cikin takardar, NAN ta ce, "Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya canja shugabannin tsaron kasar nan da wasu sababbi masu burin yi wa kasa aiki, musamman shugabannin soji.

KU KARANTA: Sojin sama sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu

"Zaben da zai sake na shugabannin ya zama musamman don kwarewa da samar da salo iri-iri na yakar 'yan ta'adda, musamman wadanda zasu kawo dabaru na daban don kawo karshen 'yan Boko Haram.

"Sannan wajibi ne a mayar da hankali wurin gano tushen matsalar da ke kawo cikas ga tsaron Najeriya.

"Muna yi wa gwamnatin tarayya tuni a kan cewa hakkinsu ne kula da rayukan al'umma da dukiyoyinsu."

A wani labari na daban, wani mai fadi aji a jam'iyyar APC, Julius Ihonvbere, ya ce har yanzu shugaba Buhari bai nuna alamar goyon bayan Goodluck Jonathan ba a kan kara tsayawa takara.

Idan ba a manta ba, Legit.ng ta bayyana rahotonni sun nuna yadda APC take kokarin gamsar da Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya, ya tsaya takara a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel