Buni: APC zata jijjiga siyasar Nigeria da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba

Buni: APC zata jijjiga siyasar Nigeria da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba

- Jam'iyyar APC ta karbi gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, wanda ya fita daga jam'iyyar PDP

- Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce da sauran mamaki nan gaba kadan

- A ranar Laraba ne Sanata Ishaku Abbo, daga jihar Adamawa, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, ya ce "Jam'iyyar APC nan bada jimawa ba za ta jijjiga siyasar Najeriya da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba a ƙasar"

Jam'iyyar APC zata fuskanci karɓar mutane masu sauya sheƙa daga jam'iyyu mabambanta zuwa APC a satattuka masu zuwa, a cewar Mai Mala Buni.

Mala Buni, wanda shine shugaban kwamitin riko na APC mai kula da tsare - tsare, ya faɗi hakan ne yayin wani taro da manyan jam'iyya a ranar Laraba.

Maganar tasa ta zo awanni kaɗan bayan Sanatan jihar Adamawa, Elisha Abbo, ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

KARANTA: Majalisa ta amince da bukatar Buhari ta sakin N148bn a matsayin biyan bashi ga wasu jihohi hudu

Ya kuma zo satuttuka kaɗan bayan gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

Buni: APC zata jijjiga siyasar Nigeria da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba
Buni: APC zata jijjiga siyasar Nigeria da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba
Asali: UGC

Mutane biyun da suka sauya sheƙar zuwa APC sun bayyana cewa rashin adalci da riƙon sakainar kashi da al'amuran jam'iyyar PDP sune maƙasudin sauya sheƙar tasu.

Da yake jawabi, gwamna Buni ya ce kwamitin jam'iyyar ya sulhunta kusan dukkan rikice-rikicen cikin gida na APC a jihohin da take da mulki.

KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas

Ya lissafo sunayen mutanen da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar baya baya nan wanda suka haɗa da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Barnabas Gemade, tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Gwamna Umahi da sauran mutane wanda suka dawo jam'iyyar.

Ya ce ƴan Najeriya su tsammaci dawowar wasu manya-manya da dama zuwa jam'iyyar APC.

"Akwai irinsu da yawa waɗanda suka nuna muradinsu na son dawowa ko sauya sheƙa zuwa jam'iyyar," a cewarsa.

"A taƙaice, ina son tabbatar muku da cewa nan bada daɗewa ba, jam'iyyarmu ta APC zata jijjiga hazon siyasar Najeriya.

"Za ta karɓi mutanen da a tarihin siyasar ƙasar nan bai taɓa gani ba, da yardar Ubangiji, Jam'iyyar APC, za ta cigaba da jagorantar siyasar ƙasar nan."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel