Sojin sama sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu

Sojin sama sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu

- Rundunar sojin sama tana kara samun nasarori da dama a hare-haren da take kai wa 'yan ta'adda

- A ranar Asabar, rundunar ta kai hari Ngwuri Gana, da wuraren Gulumba Gana-Kumshe, kusa da tafkin Chadi

- Rundunar ta samu nasarar kashe 'yan Boko Haram da dama, sannan ta lalata maboyarsu ta jiragen sama

A ranar Asabar, sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar maboyar 'yan Boko Haram da dama.

Kamar yadda wata takarda wacce kakakin rundunar 'yan sojin, John Enenche ya sa hannu, rundunar sojin sama sun yi wata ragargaza a ranar Juma'a, inda sabuwar rundunar da aka kirkira karkashin Operation Lafiya Dole, mai suna 'Wutar Kabir II' ta aiwatar da harin.

Sai da sojojin sama suka tabbatar da maboyar 'yan ta'addan sannan suka fara ragargazarsu, Channels TV ta wallafa.

Sojin Najeriya sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu
Sojin Najeriya sun ragargaza mayakan ISWAP a Borno, sun watsa maboyarsu. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

Kamar yadda takardar tazo, "Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole, ta samu nasarar ragargazar maboyar 'yan Boko Haram da dama da ke Ngwuri Gana, kusa da wuraren Gulumba Gana-Kumshe, har da na Tumbuma Baba kusa da tafkin Chadi, duk a arewacin Najeriya, jihar Borno."

"A hari na musamman da rundunar sojin sama ta kai maboyar 'yan Boko Haram ta jiragen sama ta samu babbar nasara. Hakan ya yi sanadiyyar kashe 'yan Boko Haram da dama," yace.

KU KARANTA: Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa a gonar Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno, inda yace 'yan ta'addan basu da hankali.

"Na yi matukar takaicin kisan manoma masu kwazo da 'yan ta'adda suka yi a jihar Borno. Kowa a kasar nan ya ji takaicin wannan kashe-kashe na rashin hankali. Ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalan wadanda aka kashe, ina musu addu'ar samun rahama."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel