Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari

Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa 40 na Maiduguri

- Ya bayyana takaicinsa karara, inda yace gyara tsarin tsaron Najeriya yana daukar dogon lokaci kuma hakan bai kamata ba

- Atiku ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda aka kashe, yana mai yi wa mamatan fatan samun rahama

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar , ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, kuma ya yi kira ga jami'an tsaro da su yi gaggawar gyara tsarin harkar tsaro a kasar nan.

Atiku ya yi wannan kiran ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, jaridar The Punch ta wallafa.

Dan takarar shugaban kasa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019, ya bayyana yadda al'amarin ya bashi tsoro inda yace bai san yadda zai bayyana tashin hankalin da ya shiga ba.

Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari
Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

Kamar yadda ya wallafa, "Jikina ya yi sanyi. Ban san kalaman da zan yi amfani da su ba. Ya kamata a ce rayukan 'yan Najeriya sun fi haka daraja.

"Canza tsarin tsaron kasar nan yana daukan dogon lokaci. Muna musu fatan samun rahama, sannan muna yi wa iyalansu ta'aziyya."

KU KARANTA: Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Olaide Oluwo, tana bukatar a yi mata adalci bayan wani sojan Najeriya da ke Sangotedo, jihar Legas ya ci zarafinta a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda ta wallafa bidiyonta a kafar sada zumuntar zamani, wanda tace ya ci zarafinta ne saboda ba ta gaishesu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng