Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa

Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa

- Ni ce kadai budurwar da ta fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta sanar da kowa ba, cewar wata budurwa

- Budurwar, mai sayar da kaji a kasuwar Afia Abakpa da ke jihar Enugu, ta bayyana abubuwan alfahari da take da su

- Ta ce ga duk mai shirin siyan kaji don shagulgulan karshen shekara, zai iya garzayawa ya siya a wurinta

"Nice kadai budurwar da ta fita da saurayinta har ta kashe masa N7000 ba tare da na fadi wa kowa ba," cewar wata budurwa.

Budurwar mai karancin shekaru, ta yi wannan wallafar a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda take bayyana abubuwan alfahari dangane da ita.

Budurwar mai sayar da kaji a kasuwar wuraren Abakpa Nike da ke jihar Enugu, ta tallata hajar ta a Facebook, inda tace za su siyan kajin wurinta don shagulgulan karshen shekara.

Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa
Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa. Hoto daga Onuh Chisome Maryjane
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

A cikin alfaharin da tayi, tace "Nice wannan kyakkyawar yarinyar Okuko wacce ku ka sani. Yarinya mai kifi, mai ayaba."

Tace, "Ni ce kadai budurwar da ta fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta sanar da kowa ba.

"Ina yanka kaji in samu kudi. Ina zaune a kasuwar Abakpa da ke jihar Enugu. Za ku iya zuwa ku duba. Idan kun zo shagalin bukukuwan karshen shekara, ku garzayo ku siya kaji na."

KU KARANTA: Gwamnan APC ya fatattaki jami'an gwamnatinsa 2 a kan kin bin ra'ayinsa

A wani labari na daban, an umarci John Njoroge ya dakata da shirye-shiryen aurensa da Rose Wanjiku, (ba sunayensu na asali ba), bayan ya turo magabatansa, The Nation ta wallafa.

Al'amarin ya daga wa Njoroge hankali, bayan ya gano cewa ubansu daya da Wanjiku domin diya ce ita ga kishiyar mahaifiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng