Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a

Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a

- Tawagar wakilan fadar shugaban kasa sun ziyarci yankin kudu maso kudu a cigaba da ziyarar sassan Nigeria

- Bayan taron tattaunawarsu da shugabannin yankin a garin Fatakwal na jihar Ribas, gwamna Nyesom Wike ya tattauna da manema labarai

- A cewar Wike, shugaba Buhari zai cinnawa Nigeria wuta matukar ya gaza biyan bukatun jama'a

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya shawarci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a kan ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa a shirye yake ya biya musu buƙatunsu.

Wike ya ce shugaban ƙasar zai jawo ƙasa ta kama da wuta idan har yaƙi biyan buƙatun roƙon da shugabannin al-umma.

Shugabanni sun yi roƙon a biya musu buƙatun al-ummarsu yayin wata tattauna da ƙusoshin fadar shugaban ƙasa.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, shine ya jagoranci tattaunawar.

KARANTA: El-Rufa'i ya fadi rukunin 'yan arewa da ke adawa da gyara da sauye-sauye a mulkin kasa

Jaridar Punch ta rawaito cewa Gambari ya jagoranci ministoci da masu zartar da doka tattaunawa da shugabannin yankunan siyasa shida na Najeriya.

Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a
Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a
Asali: UGC

An yi taron ne don tattauna hanyoyin farfarɗowa da nuna kulawar gwamnatin tarayya bayan ta'annatin da aka fuskanta a kasa sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

Gambari da tawagarsa sun haɗu da gwamnoni da shugabannin siyasar yankin kudu maso kudu a Port Hacourt, babban birnin jihar Ribas, a ranar Talata.

Yayin taron, shugabannin kudu maso kudu da gwamnoni sun buƙaci ayi wa ƙasa garambawul daidai da ƙa'idar sahihiyar Jamhuriyya.

Acewarsu, hakan zai kawo cigaba, zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali a ƙasa baki daya.

Da yake bada bayanan yadda suka ƙarƙare taron, Wike ya ce shugaban ƙasa yana da isasshen lokacin da zai aiwatar da buƙatar al'umma kuma ya kankaro daraja da mutuncinsa.

Gwamnan ya yi magana ranar Alhamis a gidan talabijin na Channels a wata hirar yau da kullum wadda jaridar Punch ke kula da ita.

KARANTA: Ganduje ya bayar da umarnin sauya wa gidan Zoo matsuguni daga cikin birni

Ya ce,"ni ba mutumin banza bane. Ban yarda cewa saboda ka gaza yin abin daka alƙawarta a jiya ba, ace wai bazaka yi abin daka alƙawarta a yau ba.

Koda shi Buhari bai cikawa ƴan Najeriya alƙawuran da ya ɗaukar musu ba, zai iya cewa, kunga, jiya nayi muku alƙawari, amma ban cika ba, kuma hakan yana taɓa min kimata, saboda haka albarkacin mutanen da suka sanni, zan cika alƙawarin da nayi.

"Na yarda cewar idan har shugaba Buhari ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka a irin damar da ya samu a halin yanzu, zai cinnawa Najeriya wuta."

Wike ya kalkale da cewa ''zummar cikawa mutane buƙatarsu shine muhimmi a siyasa.''

Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, ya ce "Jam'iyyar APC nan bada jimawa ba za ta jijjiga siyasar Najeriya da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba a ƙasar"

Jam'iyyar APC zata fuskanci karɓar mutane masu sauya sheƙa daga jam'iyyu mabambanta zuwa APC a satattuka masu zuwa, a cewar Mai Mala Buni.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel